Latest
Kungiyar Progressive League of Youth Voters ta zargi Rabiu Kwankwaso da rubuta wasika ga 'yan Majalisar Tarayyar NNPP domin caccakar Bola Tinubu kan masarautun Kano.
'Yan bindiga sun kai hari gidan wani malamin jami’ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) da ke Katsina. An ce 'yan ta'addan sun kashe malamin, sun kuma tafi da yaransa biyu.
Dillalan man fetur a Najeriya sun nuna fargabar cewa da yiwuwar ba za a samu saukin da ake tsammani a fetur ba idan matatar Ɗangote ta shigo da nata kayan kasuwa.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Adolphus Wabara ya bayyana cewa an turo masa kudi N250m domin ya amince da tarace da Olusegun Onasanjo ya nema a 2006.
Ana fargabar sabon rikicin siyasa ya sake kunno kai a cikin jam'iyyar APC bayan da Sanata Kabiru Marafa ya farfado da tsagin jam'iyyar da ya ke jagoranta a Zamfara.
Ministan Ilimi a Najeriya, Farfesa Tahir Mamman ya bukaci kungiyoyi masu zaman kansu su yi koyi da Dakta Emeka Offor wajen tallafawa harkar ilimi a Najeriya.
Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa an samu karuwar wadanda suka rasu a harin da 'yan ta'adda su ka kai Gwoza, yayin da wasu mutane 20 su ka rasu.
Dakarun hadin gwiwa na kasashe masu yaki da Boko Haram (MNJTF) sun fatattaki maboyar miyagu a iyakokin kasar nan da Kamaru da tafkin Chadi, kuma sun yi nasara.
Yayin da ake kokarin gyaran fuska a dokar masarautun jihar Sokoto, yau Talata za a fara sauraran ra'ayin jama'a game da sabuwar dokar da ake magana a kai.
Masu zafi
Samu kari