Latest
Farfesa Umar Labdo ya ce Rabiu Musa Kwankwaso ya nada Muhammadu Sanusi II ne tun 2014 saboda gabar siyasa da kuma neman batawa Goodluck Jonathan rai.
Gwamnan jihar Benuwai, Rabaran Hyacinth Alia ya sanar da sa dokar zaman gida a ƙaramar hukumar Ukum da kewaye biyo bayan ɓarkewar zanga-zanga a yankin.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar babban ɗan tsohon gwamnan jihar Oyo, Cif Kolapo Ishola mai suna Kunle Kolapo a yau Laraba 3 ga watan Yulin 2024.
Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi karin haske kan tattaunawa da ya yi da gwamnonin kudu, ya ce ba su yi magana kan sake Nnamdi Kanu ba.
Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta rahotannin da aka yada kan kai harin kunar bakin wake a titin hanyar Kaduna zuwa Abuja. Ta ce babu gaskiya a rahotannin.
Majalisar dattijan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta sauya salon tunkarar ƴan tada kayar baya domin magance hare-hare irin wanda aka kai Gwoza a Borno.
Wani matashi mai suna Ufuoma Umurie ya hallaka mahaifinsa wanda babban Fasto ne mai suna Isaac Umurie yana tsaka da bacci a jihar Delta a yau Laraba.
Rundunar yan sanda a jihar Rivers ta kama shugaban yan banga mai suna Felix Nwaobakata dauke da kokon kai da kasusuwan mutane bayan ya yi kisan kai.
Tsohon kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Hon. Yakubu Dogara ya fayyace komai kan kuɗin da mambobin suke samu ba kamar yadda ƴan Najeriya ke zargi ba.
Masu zafi
Samu kari