Latest
Wani bene mai hawa biyu da ya zama kango ya rufto kan mutane a jihar Osun. Mutum 5 sun makale yayin da masu aikin ceto ke kokarin ganin sun kubutar da su.
Shugaban Bola Tinubu na Najeriya ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa tsohon shugaban Amurka, Donald Trump inda ya ce wannan lamari abin takaici ne.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya nuna farin cikinsa bisa dawowar tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim zuwa APC.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare kan bayin Allah a jihar Anambra. 'Yan bindigan sun hallaka mutum daya tare da sace wasu mutum hudu.
A yayin da ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta duba bukatun matasan Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya ba da shawarwari guda shida kan zanga-zangar lumana.
Malamin gargadiya, Satguru Maharaj Ji a jihar Osun ya bukaci Gwamna Ademola Adeleke ya tuge sarkin Iwo, Oba Abdulasheed Akanbi daga sarautar garin.
Gwamnatin jihar Filato ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku domin karrama wadanda suka mutu a sakamakon ginin makaranta da ya rufta a garin Jos.
Shugaban hukumar yaki da hanci ta EFCC, Ola Olukoyede ya fasa kwai kan yadda wasu malaman addini ke cin hanci fiye da sauran masu rike da mukaman siyasa.
Hukumar kwastam ta Najeriya ta yi asarar daya daga cikin jami'anta a jihar Jigawa. Jami'in ya rasa ransa ne bayan wani dan fasa kwauri ya buge shi da mota.
Masu zafi
Samu kari