Latest
Kungiyar matasan CAN a jihar Taraba ta ba da umarnin gudanar da addu'o'i da azumi na tsawon kwanaki uku yayin amfanin gona suka fara lalalcewa a fadin jihar.
Babban malamin addinin Kirista, Fasto Enoch Adeboye ya caccaki matan da ke yin kwalliya a lokacin aurensu yana mai cewa irin wadannan matan wawaye ne.
Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya fito ya yiwa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, wankin babban bargo kan sukar da ya yiwa Bola Tinubu.
Ana fama da tsadar rayuwa, kakakin matasan PDP na kasa, Dare Akinniyi, ya bukaci Tinubu da ya sake duba manufofinsa na tattalin arziki da hada kai da ‘yan adawa.
Wani matashin mai suna Maleek Anas ya wallafa a shafin X cewa ya sayi buhunan siminti guda biyu kan kudi N6,000 kowane daya daga kamfanin Dahiru Mangal.
Kungiyar SERAP ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya sa a binciki gwamnonin Najeriya kan bashin da suka karbo daga hannun bankin duniya.
Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kaddamar da shirin samar da gidaje karkashin 'Renewed Hope'. Mun kawo matakan mallakar gida a wannan tsarin.
Hukumar NYSC ta gargadi masu shafukan yanar gizo daga rubuta labaran karya kan lamuran hukumar bayan da ta karyata cewa za a fara biyan 'yan bautar kasa N70,000.
Dan Majalisar Tarayya a Kano, Abdulmumin Jibrin ya bayyana takwaransa a Majalisar Wakilai, Alhassan Doguwa a matsayin barazana ga zaman lafiyar jihar.
Masu zafi
Samu kari