Latest
Shugaban jam'iyyar APC mai adawa a jihar Oyo, Barista Isaac Ajiboye Omodewu, ya rasu. Shugaban na APC ya rasu ne a safiyar ranar Litinin, 19 ga watan Agustan 2024.
Miyagun 'yan bindigan da suka yi garkuwa da jami'in dan sanda a jihar Plateau sun hallaka shi. An gano gawar jami'in tsaron a cikin daji a ranar Lahadi.
Mazauna Gatawa da ke a Sabon Birni, jihar Sokoto sun mika lamuransu ga Allah yayin da suka dukufa da yin addu'o'in kubutar Sarkin Gobir daga hannun 'yan bindiga.
Tsohon mai ba Rabi'u Musa Kwankwaso shawara kuma dan majalisar wakilai ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC. Sanata Barau Jibrin ne ya karbe su a Abuja.
Mazauna Kano sun cika da takaicin yadda wata baiwar Allah da yaranta biyar su ka rasa rayukansu a Karkari da ke Gwarzo a jihar bayan cin tubani da ake hada da dusa.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa tsare-tsaren ci gaba da ya kawo sun sanya yana samun kiraye-kiraye na barazana daga wasu boyayyun mutane.
Wani bincike ya gano cewa fadar shugaban kasa ta yi birin da.majalisar dokokin kasar nan wajen sayowa shugaba Bola Ahmed jirgi ba tare da sahalewarta ba.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara zuwa kasar Faransa a ranar Litinin. Shugaban kasan zai dawo gida bayan ya kammala zamansa a kasar.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram. Sojojin sun hallaka wani babban kwamandan kungiyar da wasu mutum biyu a wani samame.
Masu zafi
Samu kari