Latest
Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a fuskanci hazo da ruwan sama a wasu jihohin Najeriya daga ranar Litinin, 11 zuwa Laraba 13 ga watan Nuwamba.
Dan majalisa AbdulMumin Jibrin Kofa ya bijirewa takwarorinsa na Arewa kan sabon kudurin haraji da shugaba Bola Tinubu ya bijiro da sji a kasar nan.
Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare ta sama kan maboyar 'yan bindiga a jihar Katsina. Sojojin sun samu nasarar hallaka masu yawa daga ciki.
Kungiyar MBF ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya maido tallafin man fetur a Najeriya lura da yadda miliyoyin yan kasa suka shiga mugun talauci da wahala.
Zababben gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya nada Fred Itua a matsayin Babban Sakataren Yada Labarai don inganta sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.
Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam'iyyar NNPP ya caccaki tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso kan ziyartar gwamnan Abia.
A jihar Kano, hauhawar farashin man fetur ya sa mazauna garin canza hanyar sufuri. An ce yanzu sun koma tafiya a kasa, hawa kekuna ko amfani da babura masu lantarki.
Fadar shugaban kasa ta yi martani ga Atiku Abubakar kan wasu malamai da ya yi a kan Bola Tinubu. Gwamnatin tarayya ta ce Atiku na yi wa Bola Tinubu hassada.
An samu matsala a Sakkwato bayan yan ta'addan Lakurawa sun gano lagon daukar wasu daga cikin matasan jihar a matsayin sababbin yan ta'adda domin karfafa ayyukansu.
Masu zafi
Samu kari