Latest
Majalisar dokokin jihar Kano ta buƙaci sanatoci da ƴan majalisar wakilai na tarayya su haɗa kai su yaƙi sabon kudirin sauya fasalin harajin Bola Ahmed Tinubu.
Wani jigon PDP, David Itopa ya hango karshen gwamnatin Bola Tinubu idan jam'iyyun adawa suka hada kai. Itopa ya nuna kyakkyawan fata a kan hadewar Atiku da Obi.
Watan Disamba na dauke da bukukuwa daban-daban, daga Kirsimeti da ranar dambe zuwa daren sabuwar shekara. Mutane na sada zumunci, da tuno da al'adun gargajiya.
Wata kotun tarayya ta kori karar da PDP ta shigar da dan takarar APC kuma gwamnan jihar Ondo. Kotun ta ce PDP ta yi jinkirin shigar da karar inda ta saba dokar zabe.
Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya yi magana kan matsalolin da suka hana kananan hukumomi ci gaba. Ya ce daga cikinsu akwai cin hanci.
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya gabatar da kasafin N382.5bn ga majalisar dokokin jiha, yana mayar da hankali kan cigaban tattalin arziki da jin dadin al'umma.
Yan sandan kasar nan sun yi tir da rahoton Amnestyu Int'l. Kungiyar ta zargi 'yan sanda da kisan masu zanga zanga. Rundunar ta fadi yadda jam'anta su ka yi aiki.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya bude sabon asibiti, wurin koyon sana'a da wurin tiyata da kula da lafiyar ido a kauyen Tudun Biri bayan shekara guda.
'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane masu yawa bayan sun kai hari a jihar Sokoto. Miyagun 'yan bindigan sun kuma hallaka wasu mutane tare da raunata wani daban.
Masu zafi
Samu kari