Latest
An samu asarar rayuka sakamakon wani hatsarin jirgumin ruwa da ya auku a jihar Benue. Jirgin ne dai ya gamu da hatsarin ne bayan an cika masa kaya.
Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa am bar Arewa a baya a fannin ci gaba, ya ce idan aka raba Najeriya yankin na tsaka mai wuya.
Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu, ya amsa tabbas yana da alaka da jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya. Kawu ya ce NNPP ce ta sa shi yin alaka da APC.
Tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi ya magantu bayan cire shi a mukaminsa inda ya ce yana tare da Gwamna Abba Kabir.
Sheikh Daurawa ya ce rashin Sallah, shaye-shaye, rashin makaranta, da kin biyayya ga iyaye suna daga cikin alamomin matashin da ke shirin lalacewa cikin al'umma.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta fito ta musanta cewa ta ba Goodluck Jonathan tikitin yin takara a zaben shugaban kasa na shekar 2027 da ke tafe.
Mawaki Abdul Respect ya angwance da Hassana Abubakar a Kano. Shahararrun mawaka da jarumai kamar Ado Gwanja, Momee Gombe, da Ali Nuhu sun halarci bikin.
Tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege da Hon. Erhiataka Suenu-Ibori sun bugi kirji inda suka yi alkawarin mayar da Delta jihar APC.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan miyagun 'yan bindiga a jihar Taraba. Sojojin sun kuma yi nasarar kubutar da wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su.
Masu zafi
Samu kari