Jarumin Kannywood Ya Gigice da Rahama Sadau Ta Yi Masa Kyauta Ta ban Mamaki
- Rahama Sadau ta yi wa jarumi Yusuf Lazio kyautar da ta gigita shi, ya bayyana cewa ba a taba yi masa kyauta mai girma irin wannan ba
- Yusuf Lazio ya bayyana wa duniya cewa ya dauki Rahama a matsayin uwa, inda ya jinjina mata bisa wannan kyauta ta musamman da ta yi masa
- Mabiyan Lazio sun yi wa Rahama godiya duk da cewa ba su san irin kyautar da aka yi masa ba, amma sun yaba da karamcin jarumar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Ya zuwa yanzu, Rahama Sadau ta sake tabbatar da kirarin da ake yi mata, na zama "Lailatul Kadarin 'yan Kannywood" a fagen kyautatawa 'yan masana'antar.
A yayin da ake bikin karamar Sallah, fitacciyar 'yar wasan Hausa, Rahama Sadau, ta yi wa jarumi kuma mawaki, Yusuf Lazio kyautar da ta gigita shi.

Asali: Instagram
Rahama Sadau ta yi wa Lazio babbar kyauta
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Instagram, Yusuf Lazio ya ce kyautar da Rahama ta yi masa, ta yi matukar girgiza shi, kasancewar bai taba tsammanin haka daga gare ta ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yusuf Lazio, wanda ya fito a fina finan Hausa da dama, ciki har da Gidan Sarauta, Na Ladidi da sauransu, ya ce Rahama ta yi masa kyautar da ba a taba yi masa irinta ba.
Domin kara tabbatar da girman sha tara ta arzikin da Rahama ta yi masa, Yusuf Lazio ya jaddada cewa,
"yau kin yi mun abin da ban yi tsammani ba."
Sanarwar Yusuf Lazio ta ce:
"Tabbas kin dauke ni ďa kamar yanda na dauke ki uwa, @rahamasadau yau kin yi mun abin da ban yi tsammani ba, kin yi mun abin da ba a taba yi mun ba.
"Ba ni da kalmar da zan yi amfani da ita wajen godiya kuma ba ni da abin da zan ba ki a matsayin tukuici.

Kara karanta wannan
'Yadda watsi da shirin Sardauna ke jawo asarar rayukan Hausawa,' Yan kasuwa kan kisan Edo
"Wannan zuri’a tabbas mutanen kirki ne, Allah ya tsare ku a duk inda ku ke."
Lazio ya yi wa Rahama Sadau addu'o'i
Ba iya Rahama ta samu yabo da addu'o'i daga Yusuf Lazio ba, hatta kannanta sun shiga cikin wadanda jarumin ya jinjinawa kan kyautar da ya samu.
Lazio ya kara da cewa:
"Ya Allah, albarkacin wannan azumi da muka gama, ya Allah albarkacin Annabi (SAW) da Alkur’ani, ya Allah albarkacin kyawawan sunayenka guda dari ba daya.
"Allah ya raba ki da duniya lafiya, Allah ya sa ki gama da iyayenki lafiya, Allah ya biya miki bukatunki na alkairi, Allah ya kara hada kanki da yan uwanki, Allah ya rabaki da sharrin mutun da aljan, Allah ya ba ki miji na gari @rahamasadau."
Mabiyan Lazio sun jinjinawa Rahama Sadau

Asali: Instagram
Mabiyan jarumin a shafinsa na Instagram, su ma sun yi wa Rahama Sadau godiya duk da cewa ba su san kyautar da aka yi wa Lazio ya ke shi wa Rahama albarka ba.
realabmaishadda:
"Allah ya saka mata da alkhairi, Man Lazee na hakimin Dabe."
madam__korede:
"Lazio kawai ka ce ka kwace min gwamnatin tarayya di ta."
Lazio ya yi saurin ba ta amsa da cewa:
"@madam__korede, a haba madan, wa ne ni, ni na isa? Ai ke ta gaban goshi ce."
Yadda wasu 'yan wasan Kannywood ke fama
'Yan wasan masana'antar Kannywood na fuskantar matsaloli musamman na kudi inda wasu jarumai ke korafin karancin kudin shiga.
Ladin Chima ta taba cewa a tsawon shekarunta 60 a fim, ba ta taɓa samun fiye da N5,000 a matsayin kudin sallama a fim ba.
Sai dai wasu masu shirya fina-finai sun musanta haka, suna cewa suna biyan ta fiye da hakan. Annobar COVID-19 ta kara dagula al’amura a masana'antar, inda yawancin ‘yan wasa suka rasa ayyukan yi.
Haka nan, hukuncin da Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ta yanke na soke lasisin ‘yan Kannywood ya sha jawo janyo cece-kuce, inda wasu ke ganin ana hakan ne kawai don siyasa.

Kara karanta wannan
Hafsan tsaro ya tsoma baki kan kisan ƴan Arewa a Edo, ya fadi shirinsu kan lamarin
Duk da haka, akwai masu tallafawa juna daga fitattun mutane kamar Naziru Sarkin Waka, wanda ya taba bai wa marigayiya Ladin Chima N2m don fara kasuwanci.
Rahama Sadau ta gana da ministocin Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Rahama Sadau ta gana da ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle, domin tattauna hadin gwiwa kan shiri na musamman da ta shirya.
Haka kuma, jarumar ta gana da ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris Malagi, don tattauna batutuwan da suka shafi shirin da ya baje al'adun Hausa.
Shirin Arewa Turn Up, wanda Rahama ke jagoranta, muhimmin taro ne da ke baje kolin al’adun Arewa da haɓaka fasahar yankin, kuma irinsa na farko daga yankin.
Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng