Soshiyal Midiya: Jaruman Kannywood 10 da Suka Fi Yawan Mabiya a Facebook, Instagram

Soshiyal Midiya: Jaruman Kannywood 10 da Suka Fi Yawan Mabiya a Facebook, Instagram

Jaruman masa'antar Kannywood suna amfani da shafukan sada zumunta wajen tallace tallace, dora hotuna da bidiyo da kuma tattaunawa da masoyansu na fadin duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Duk da cewa akwai jaruman fina finan Hausa da ba su amfani da soshiyal midiya, amma mafi akasari suna da shafuka a Facebook, Instagram, Twitter da kuma Tiktok.

Jerin jaruman Kannywood mafi yawan mabiya a shafukan sada zumunta
Ali Nuhu ne a kan gaba a jerin jaruman Kannywood mafi yawan mabiya a soshiyal midiya. Hoto: Hadiza Aliyu, Actoralinuhu, Rahama Sadau
Asali: Facebook

Legit Hausa ta tattaro maku jerin jaruman Kannywood 10 da suka fi yawan mabiya a shafukan sada zumunta a 2024.

Jaruman Kannywood da yawan mabiyansu

10. Maryam Booth (Dijangala)

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maryam Booth, diya ga marigayiya Zainab Booth, kuma 'yar uwa ga Amude da Ramadan Booth, ta samu daukaka tun bayan fitowa a shirin Dijangala tare da jarumi Adam A Zango.

Kara karanta wannan

Bidiyon Bello Asada: Malaman Musulunci sun yi gargadi, sun bi bayan Matawalle, Tinubu

A shafinta na Facebook, Maryam Booth tana da mabiya 448,000 yayin da ta ke da mabiya miliyan 2.1 a shafinta na Instagram da kuma mabiya 203,3000 a shafinta na TikTok.

Idan aka hada duka mabiyanta a shafukan uku, jaruma Maryam Booth za ta tashi da mabiya kimanin miliyan 2.7.

9. Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi na daya daga cikin matan Kannywood da suka shara a duniya, ta fito a manyan finanai finai irinsu, Labari Na, Sai Wata Rana, Madubin Dubawa da sauransu.

A shafinta na Twitter, Nafisa Abdullahi na da mabiya 267,200 yayin da ta ke da mabiya miliyan 2.2 a shafinta na Instagram da kuma mabiya 433,000 a shafinta na TikTok.

Nafisa Abdullahi na da jimillar mabiya kimanin miliyan 2.8 a duka shafukanta uku.

8. Maryam Yahaya

Jaruma Maryam Yahaya ta fara yin shuhura a masana'antar Kannywood bayan yaduwar wakar 'Abin da ya ke raina' inda ta fito tare da mawaki kuma jarumi Umar M. Shareef.

Kara karanta wannan

An soki Barau Jibrin kan karbar mutane zuwa APC alhali ana kukan kuncin rayuwa

A shafinta na Instagram, Maryam Yahaha na da mabiya miliyan biyu yayin da ta ke da mabiya sama da 900,000 a shafinta na TikTok.

Idan aka hada jimillar mabiyan Maryam Yahaya na shafukan biyu, tana da kimanin mabiya miliyan uku.

7. Umar M Shareef

Umar M. Shareef ya fara yin shuhura a fannin waka, kafin daga bisani ya fara fitowa a fina finai kamar su Gidan Saurata, Sareena Madubin Dubawa, Hafeez da dai sauransu.

A shafinsa na Facebook, Umar. M Shareef na da mabiya miliyan 1.3 yayin da ya ke da mabiya miliyan 1.6 a shafinsa na Instagram da kuma mabiya 852,500 a shafinsa na TikTok.

A shafinsa na Twitter Umar M Shareef na da mabiya 119,700 wanda ya sa ya hada jimillar mabiya kimanin miliyan 3.8 a duka shafukan hudu.

6. Aisha Humaira

Aisha Humaira jaruma ce, mai shirya fina finai kuma daya daga cikin na hannun daman mawaki Dauda Kahutu Rarara inda ake yawan ganinta a wakokin siyasa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda jarumin Nollywood ya koma sana'ar gyaran famfo a ƙasar Kanada

A shafinta na Instagram, Aisha Humaira na da mabiya miliyan biyu yayin da ta ke da mabiya miliyan 2.1 a shafinta na TikTok.

Aisha Humaira na da jimillar kimanin mabiya miliyan 4.1 a shafukan nata biyu.

5. Adam A Zango

Adam A. Zango (Usher) ba boyayye ba ne a duniyar fina finan Hausa. Mawaki kuma jarumi Zango ya taka muhimmiyar rawa wajen raya masa'antar Kannywood har ta kawo yanzu.

A shafinsa na Facebook, Adam A. Zango na da mabiya 924,000 yayin da ya ke da mabiya miliyan 1.6 a shafinsa na Instagram da kuma mabiya miliyan 1.7 a shafinsa na TikTok.

A jimillatance, jarumi Adam A Zango na da mabiya kimanin miliyan 4.3 a duka shafukan uku.

4. Naziru Ahmed (Sarkin Waka)

Naziru Ahmed, wanda aka fi sani da sarkin wakar sarkin Kano, fitacce ne a masana'antar fina-finai kasancewar mawaki kuma mai daukar nauyin fina finan.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

A shafinsa na Facebook, Naziru Ahmed na da mabiya miliyan 1.6 yayin da ya ke da mabiya miliyan 1.9 a shafinsa na Instagram da kuma mabiya 814,100 a shafinsa na TikTok.

Mawaki Naziru na da kimanin mabiya miliyan 4.3 a duka shafukansa na soshiyal midiya.

2. Hadiza Gabon

Hadiza Gabon ta kasance fitatta jaruma a masana'antar Kannywood wadda ta fito a manyan shirye shirye, na baya bayan nan shi ne shirin kamfanin Amart na Mayan Mata.

A shafinta na Facebook, Hadiza Gabon na da mabiya miliyan 1.6 yayin da ta ke da mabiya miliyan 2.8 a shafinta na Instagram da mabiya miliyan 1.5 a shafinta na TikTok.

Jaruma Hadiza Gabon na da mabiya N500,100 a shafinta na Twitter, wanda ya sa ta samu jimillar mabiya miliyan 6 a duka shafukanta hudu.

2. Rahama Sadau

Jarumar Kannywood, Nollywood da kuma Bollywood, Rahama Sadau ta samawa kanta suna a duniyar fina finai inda ta zama daya daga cikin jaruman Hausa da aikinsu ya je ketare

Kara karanta wannan

An gaji: Lokuta 3 da jama'ar gari suka aukawa miyagun 'yan bindiga

A shafinta na Facebook, Rahama Sadau na da mabiya miliyan 1.3 yayin da ta ke da mabiya miliyan 3.3 a shafita na Instagram da kuma mabiya 582,3000 a shafinta na TikTok.

Jarumar na da mabiya miliyan 1 a shafinta na Twitter, wanda ya sa ta tara jimillar mabiya miliyan 6.1 a shafukanta na soshiyal midiya.

1. Ali Nuhu

Ba abin mamaki ba ne Ali Nuhu ya kasance wanda ya fi yawan mabiya a shafukan sada zumunta a cikin jaruman masana’antar ta Kannywood, kasancewarsa 'Sarki.'

A shafinsa na Facebook, Ali Nuhu na da mabiya miliyan 3.5 yayin da ya ke da mabiya miliyan 3 a shafinsa na Instagram da mabiya miliyan 1.3 a shafinsa na TikTok.

Jarumi Ali Nuhu na da mabiya 485,600 a shafinsa na Twitter wanda ya sa ya samu jimillar mabiya miliyan 8.5 a dukkanin shafukansa hudu.

Jarumi ya fice daga NNPP

Kara karanta wannan

Jerin jihohin Arewa da aka fi yawan sace mutane cikin shekara 1 a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawaki Ali Isah Jita ya sanar da ficewarsa daga tafiyar jam'iyyar NNPP a jihar Kano zuwa jam'iyyar APC.

Ali Jita ya hakura da tafiyar Kwankwasiyya inda ya koma APC ta hannun mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin Maliya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.