Dalilin da ya hana jaruma Maryam Yahaya aure

Dalilin da ya hana jaruma Maryam Yahaya aure

- Shahararriyar jarumar Kannywood, Marayam Yahaya ta bayyana dalilin da yasa bata yi aure ba har yanzu

- A cewar jarumar, rashin mijin aure ne ya kawo mata wannan tsaikon

- A kwanakin baya ne Abubakar Bashir Maishadda ya bayyana cewa, Allah ne bai yi aurensa da jarumar ba

Shahararriyar jarumar fina-finan hausa, Maryam Yahaya ta bayyana dalilin da ya hanata aure.

Jarumar ta bayyana hakan ne a hirar da tayi da gidan rediyo na Freedom dake Kano.

Jarumar tace: "Da aure da mutuwa duk lokaci ne, idan lokaci kuwa yayi ai zan daga. Baabu mijin ne, hakan ne ya hanani auren. Ku fito ku aureni, kunsan aure maza yanzu wuya suke."

KU KARANTA: Masan'antar Kannywoood tayi sabbin shuwagabanni masu tace fina-finai

A kwankin baya ne dai hotuna suka dinga yawo a kafafen sada zumunta ana cewa, an kasa Maryam Yahaya don kuwa saurayinta Maishadda zai angwance da matashiyar jaruma Hassana Muhammad.

Sai dai, a wata hirar da gidan rediyon Freedom yayi da Abubakar Bashir Maishadda, ya tabbatarwa da gidan rediyon cewa tabbas ya taba soyayya da Maryam.

Amma Allah ne bai nufa zai aureta ba domin yanzu haka an kusa bikinsa.

Shararriyar jarumar na daga cikin manyan jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a masana'antar ta Kannywood.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel