Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon Ta Ba ’Yan Mata Masu Shirin Shiga Fim Shawara

Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon Ta Ba ’Yan Mata Masu Shirin Shiga Fim Shawara

  • Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon ta ba yan mata masu shirin shiga harkar fim shawarar hakuri a kan shi ya fi alheri
  • Hadiza Gabon ta fadi haka ne tare da bayyana cewa akwai tarin illoli ga 'yan mata idan suka shiga masana'antar Kannywood
  • Legit ta tattauna da masanin addinin musulunci, ustaz Manga Adamu Hamza kan jin yadda Musulunci zai kalli maganar jarumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu da aka fi sani da Hadiza Gabon ta yi magana kan 'yan mata masu shirin shiga fim.

Hadiza Gabon ta ce akwai abubuwan da ya kamata yan mata su maida hankali a kai domin gina rayuwa mai kyau maimakon shiga fim.

Kara karanta wannan

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun tafka ɓarna, sun sace mutane a babban titin zuwa Kano

Hadiza Gabon
Hadiza Gabon ta ba mata shawara kan shiga fim. Hoto: @adizatou
Asali: Instagram

Jarumar ta fadi haka ne a wata hira da ta yi cikin tambaya da amsa kamar yadda shafin Bakori Celebrities ya wallafa hirar a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda suke ciki fim a halin yanzu

A cikin hirar da Hadiza Gabon ta yi, ta ce tana yiwa 'yan matan da suka riga suka fara harkar fim fatan gamawa lafiya.

Ta ce tun da sun riga sun fara ba abin da za ta musu sai fatan alheri amma tana gargadi ga masu shirin shigowa da su hakura.

Me za suyi maimakon shiga fim?

Hadiza Gabon ta ce yawanci idan yan mata suka mata tambayar neman shiga fim tana ba su shawarin yin aure ko karatu.

Ta ce yin aure ko komawa karatu shi ne abin da ya fi dacewa yan mata su yi domin gina rayuwa mai kyau a gaba.

Kara karanta wannan

Duk da dokar hana masu ciki aikin Hajji, Hajiyar Najeriya ta haifi jaririn farko a Makkah

Wane amfani ake samu a fim?

Har ila yau, jarumar ta bayyana cewa akwai amfani da ake samu a harkar fim domin ita ma ta samu daidai gwargwado.

Amma duk da haka ta ce rashin amfanin harkar yafi yawa a kan amfanin. Saboda haka ta ce yana da kyau duk wacce ta yi shirin shiga harkar ta zurfafa tunani.

Legit ta tattauna da Manga Adamu

Wani masanin addinin Musulunci, ustaz Manga Adamu Hamza ya tabbatar wa Legit cewa dama sana'ar fim ba abu bane da ya dace da mace Musulma saboda cakuduwa da ake tsakanin maza da mata.

Malam Manga ya kara da cewa maganar da jarumar ta fada gaskiya ne kuma ya kamata 'yan mata su dauki darasi daga gareta domin kaucewa fadawa cikin hadari a gaba.

Anyi ce-ce-ku-ce kan Hadiza Gabon

A wani rahoton, kun ji cewa shahararriyar jarumar Kannywood Hadiza Gabon ta saki sabon hotonta a dandalinta na soshiyal midiya kuma ya haddasa cece-kuce.

Legit ta gano cewa yayin da wasu ke yaba kyan jarumar, wasu na ganin sam rama bata yi mata kyau ba cewa ta fi a yar duma-daumar ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel