Yadda Adam A Zango zai koma sakin fina-finai bayan barin Kannywood

Yadda Adam A Zango zai koma sakin fina-finai bayan barin Kannywood

Shahararren jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta dandalin Kannywood, Adam A. Zango, ya yi karin haske dangane da matakin da ya dauka bayan ficewar sa daga masana'antar makonni kadan da suka gabata.

A ranar 15 ga watan Agustan da ya gabata ne dai fitaccen jarumin ya sanar da ficewarsa daga masana'antar, lamarin da ya ba ya da wata bukatar a sake danganta shi zuwa gare ta.

Wannan sanarwa ta Adam Zango na kunshe cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na zamani wanda ake yi wa lakabi da Instagram.

Zango dai ya bayyana cewa ya raba gari da masana'antar Kannywood daga ranar Alhamis, 15 ga watan Agusta, lamarin da ya ce zai fara cin gashin kansa domin kuwa bai dogora da masana'antar ba wajen samun arziki ko kuma sabanin haka.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jarumin ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin shugabancin kama karya da ake yi, inda ya ce shafaffu da mai a masana'antar sun fi karfi doka da ba a iya hukunta su saboda kwadayi da son zuciya.

KARANTA KUMA: Shin Boko Haram za ta kai wa kasar Afirka ta Kudu hari na ramuwar gayya

Sai dai a wani sabon sakon bidiyo da jarumin ya wallafa a shafin sa na Instagram kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, ya ce a halin yanzu zai rinka fitar da sabbin fina-finan sa ta yanar gizo, inda mabukata za su je su siya kuma su bai wa idanun su hakki.

Da yake zayyana dalilin sa, Adam Zango ya ce babu yadda za a yi mutum ya kashe makudan kudi wurin hadi ko kuma shirya fina-finai, face ya nemi hanyar da zai mayar da kudinsa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng