Dakarun Najeriya Sun Kama ’Yan Ta’adda 122, Sun Ceto Mutane 189 Cikin Mako Daya, DHQ

Dakarun Najeriya Sun Kama ’Yan Ta’adda 122, Sun Ceto Mutane 189 Cikin Mako Daya, DHQ

  • Dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar ceto akalla mutane 189 da masu garkuwa suka sace, tare da kama 'yan ta'adda 122 a cikin mako daya
  • Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana hakan, inda ta ce sojojin sun kama wasu mutane 49 da ake zargin suna satar danyen mai
  • Hedikwatar ta ce dakarunta na samun nasarori a yaki da 'yan ta'adda a fadin kasar, tana mai tabbatar da cewa an samu zaman lafiya yanzu sabanin baya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) a ranar Juma'a ta ce a cikin mako guda, sojojin da ke aikin cikin gida sun kashe 'yan ta'adda 50, sun kame 122 tare da kubutar da mutane 182 da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Alkali ya umurci a bai wa Emefiele masauki a gidan yarin Kuje

Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba a wata sanarwa da ya fitar, ya ce sojojin sun kama mutane 49 da ake zargin barayin danyen mai ne.

Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ)
Sojojin sun kama mutane 49 da ake zargin barayin danyen mai ne Hoto: Defence Headquarters
Asali: Twitter

Kazalika, dakarun sun kwato kayayyakin da barayin man suka sata da darajar su takai naira miliyan 128, jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji na samun nasara a yaki da ta'addanci - DHQ

Janar Buba ya ce, sojojin Najeriya na ci gaba da kai hare-hare kan shuwagabanni 'yan ta'adda, masu tayar da kayar baya da masu tsattsauran ra'ayi da ke zagon kasa ga tsaron 'yan kasar.

Ya ce, wannan ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda da ayyukan ta’addanci yana kara tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a kasar saboda “ana kakkabe mugayen 'yan ta'adda”.

Ya ce sojojin sun kuma kwato makamai iri-iri har guda 66 da alburusai daban-daban har guda 11,474.

Kara karanta wannan

Borno: Gobara ta yi barna a sansanin 'yan gudun hijira, mutane 2 sun mutu, gidaje 1,000 sun kone

Sojoji Sun Halaka 'Yan Ta'adda 50, Sun Kama 114

A wani labarin kuma, hedikwatar tsaro ta kasa (DHQ), ta sanar da cewa dakarun sojoji sun kashe 'yan ta'adda 50 tare da kama wasu 114 cikin mako guda.

Kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito, DHQ ta ce sojin sun samu nasara ne a ayyuka daban-daban da suka gudanar a Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso yamma.

Dakarun Sojojin Najeriya Sun Sheke Yan Ta'adda 37 a Mako 1

Wani labarin makamancin wannan, ya yi nuni da cewa, Dakarun sojoji na rundunar ‘Operation Hadin Kai’ da ‘Whirl Stroke’ sun kama wasu masu taimakawa yan ta'adda mutum huɗu a jihohin Borno da Benue.

An kama su ne a wasu ayyuka daban-daban da aka gudanar tsakanin ranakun 9 zuwa 11 ga watan Oktoban 2023, cewar rahoton Legit Hausa.

Wata sanarwa a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba, ta bakin kakakin hukumar tsaro ta ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, ya nuna cewa bayan bincike da aka yi, an kama wasu mutum uku da suke taimakawa ƴan ta'adda karɓar kuɗin fansa a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel