Jarumi Abale Zai Angwance, Katin Auren da Hoton Kyakyawar Amaryarsa Sun Fito

Jarumi Abale Zai Angwance, Katin Auren da Hoton Kyakyawar Amaryarsa Sun Fito

  • Fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood mai matukar farin jini, Adam Abdullahi Adam, wanda aka fi sani da Daddy Hikima ko Abale, zai angwance karshen makon nan
  • Kamar yadda wani kati da manyan jaruman masana'antar suka wallafa a shafukansu da yanar gizo ya nuna, jarumin zai angwance da amaryarsa a ranar Juma'a mai zuwa
  • Duk da har yanzu ma'auratan basu saki hotunansu tare kafin aure ba, sai dai, wani hoto da aka hada ya bayyana wata santaleliyar budurwa wanda mutane da dama suke tsammanin ita ce amaryar

Kano - Fitaccen jarumin masana'antar Kannywood, Adam Abdullahi Adam, wanda aka fi sani da Daddy Hikima ko Abale, zai angwance ranar Juma'a mai zuwa.

Abale Jarumi
Jarumi Abale Zai Angwance, Katin Auren da Hoton Kyakyawar Amaryarsa Sun Fito. Hoto daga @daddyhikima
Asali: Instagram

Katin daurin auren da manyan jaruman masana'antar irin su Ali Nuhu, Maryam Booth, Umar M. Sharif da sauransu suka wallafa tare da masa fatan alheri a shafukan su na Instagram ya bayyana yadda zai angwance da masoyiyarsa Maryam Farouq Sale a ranar Juma'a, 27 ga watan Janairu, 2023 da misalin karfe 1:30 na ranar Juma'a a masallacin na Uhud da ke Na'ibawa ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wajibi Ne A Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Da Wata 6: Majalisar Dattawa Tayi Ittifaki

Kamar yadda katin ya nuna:

"Iyalan Marigayi Alhaji Ado Tsakuwa da na Alhaji Umar Farouq Sale na farinciki gayyatar 'yan uwa da abokan arziki zuwa daurin auren 'ya'yansu...."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai har yanzu ba a ga hotunan da amarya da ango aka saba dauka kafin aure ba (pre-wedding pictures) kamar yadda ake ganin wasu jaruman fim na saki kafin aure ba.

Katin na dauke da hoton jarumin shi kadai, sanye da babbar riga cikin walwala da sakin fuska sanye da tabarau a fuskarsa.

Amma cikin kwanakin nan, hoton wata santaleliyar budurwa son kowa kin wanda ya rasa mai jar fata dauke da lalle a hannayenta ta ci kurus, wanda aka hada da na Abale ya yadu a shafunkan sada zumuntar zamani.

Duk da Legit.ng Hausa b ata tabbatar da sahihancinsa ba, amma jama'a sun yi amanna cewa ita ce amaryar karshen makon nan.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wani Mai Hannu a Harin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja, An Gano Abu 3

Fatanmu shi ne, Ubangiji ya sanya albarka a rayuwar aurensu da albarkatarsu da zuri'a dayyiba.

Amarya ta rasu bayan kwana 11 da aure

A wani labari na daban, wani sabon ango ya fada tashin hankali bayan amaryarsa ta kwanaki 11 ta kwanta dama.

Ya wallafa hotunan aurensa da kyakyawar budurwar cikin shigar sarauta inda ta saka alkyabba tana murmushi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel