A Karshe Yar Najeriya Ta Samu Miji Tana Da Shekaru 53, Ta Amarce Da Angonta Mazaunin Turai a Bidiyo

A Karshe Yar Najeriya Ta Samu Miji Tana Da Shekaru 53, Ta Amarce Da Angonta Mazaunin Turai a Bidiyo

  • Mafarkin wata mata yar Najeriya ya zama gaskiya yayin da ta shiga daga ciki bayan shafe shekaru da dama tana jiran tsammani
  • Sabuwar amaryar ta auri wani mazaunin Amurka tana da shekaru 53 a duniya kuma wannan shine karo na farko da take shiga daga ciki
  • Hadadden bidiyon aurensu ya bayyana a intanet kuma ya dauka hankalin mutane da dama da suka taya ta godiya ga Allah

A karshe wata mata yar Najeriya ta fita daga layin marasa aure yayin da ta amarce da sahibinta tana da shekaru 53 a duniya.

Matar mai suna Delight ta amarce da angonta mazaunin kasar Amurka wanda bai taba aure ba a rayuwarsa.

Amarya da ango a wajen daurin aurensu
A Karshe Yar Najeriya Ta Samu Miji Tana Da Shekaru 53, Ta Amarce Da Angonta Mazaunin Turai a Bidiyo Hoto: @house_of_gladio
Asali: TikTok

An gudanar da shagalin bikin ne a cocin Living Faith wanda aka fi sani da Winners Chapel.

Da yake wallafa bidiyon auren a TikTok, shafin @house_of_gladio ya ce matar ta auri mijin da Allah ya kaddara zai zama angonta.

Kara karanta wannan

Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shafin ya rubuta:

"Bayan shekaru 53 tana jiran mijin aure, Allah madaukakin sarki ya amsa addu'ar yaruwa delight. Domin a karshe ta auri mijin da Allah ya kaddara mata. Mazaunin Amurka kuma bai taba aure ba shima Allah madaukakin sarki abun godiya."

Bidiyon ya nuno lokacin da ma'auratan suka isa kan mumbarin coci domin a daura masu aure.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a a soshiyal midiya

RealJummy❤ ta ce:

"Na taya ki murna, farin cikinki zai zama madawwami yar'uwa kuma aurenki zai yi albarka da izinin Allah."

user925802534495 ya ce:

"Na taya ki murna yaruwa Allah ubangiji ya albarkaci sabon gidanki Amin ina rokon Allah ya yi mun irin haka da sunan Yesu."

winifredorji240 ya ce:

"Na taya ki murna. Aurenki ya yi albarka. Lallai Ubangiji mai aminci ne. Godiya gareka ya Ubangiji."

Kara karanta wannan

Bangarori 7 da Ake Jiran Bola Tinubu Ya Kawo Gyara Idan Ya Gaji Muhammadu Buhari

Chynatural ta ce:

"Na taya ki murna, ina rokon Allah ya yi mun irin wannan falalar, wadanda suka jira lokacin Allah ba za su taba jin kunya ba."

user7262772712556dorrian92 ta ce:

"Nima ina jiran nawa a shekaru 30 kuma ina jira cikin imani har sai Allah ya amsa mani."

Sarahcona ta ce:

"Lallai Ubangijinmu mai girma ne, Ina taya ki murna yar'uwa."

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya tarwatsa taron biki

A wani labarin kuma, wata amarya ta koka bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya ya tarwatsa shagalin taron bikin aurenta.

An gama kawata wajen taron tsaf da kayan ado kwatsam sai ga ruwan sama ya sauka lamarin da ya sa jama'a neman mafaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel