“Haka Maza Ma Suke Ji”: Budurwa Ta Mika Kokon Soyayyarta Ga Saurayi, Ya Ce Baya Yi

“Haka Maza Ma Suke Ji”: Budurwa Ta Mika Kokon Soyayyarta Ga Saurayi, Ya Ce Baya Yi

  • Wata matashiya yar Najeriya wacce ta fada tarkon soyayyar wani gaye ta tona masa sirrin da ke zuciyarta amma sai ya ki amsar tayinta
  • A wani sakon murya ta WhatsAPP, yarinyar ta ce tana ta boye soyayyar da take yi ma gayen na tsawon lokaci
  • Da ta bayyanawa saurayin sirrin da ke zuciyarta, sai ya ki karbar soyayyarta cikin wani siga mai ban dariya

Wani sakon murya na wata budurwa da ke mika kokon soyayyarta ga wani saurayi ya sa mutane da dama tofa albarkacin bakunansu.

A hirar tasu, yarinyar ta bayyanawa mutumin yadda take jin soyayyarsa a zuciyarta, tana mai nuna cewa so take su kulla alaka a tsakaninsu.

Budurwa da hirarsu da wani saurayi
“Haka Maza Ma Suke Ji”: Budurwa Ta Mika Kokon Soyayyarta Ga Saurayi, Ya Ce Baya Yi Hoto: @krakstv
Asali: Instagram

Ya ki amsa tayinta da waka

Matashiyar tana boye soyayyar da take yi wa saurayin na tsawon lokaci don haka take so ta sanar da shi ko za a dace shima yana jin ta a zuciyarsa.

Kara karanta wannan

"Ko Ba Shi Da Hannu Zan Zauna Da Shi": Labarin Zazzafar Son Da Jaruma Rakiya Moussa Ke Yi Wa Wani Mawaki Ya Girgiza Intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saurayin wanda baya jin ta a zuciyarsa ya yi watsi da tayin da ta yi masa ta hanyar tura mata shahararriyar wakar nan na sabulun opera a Najeriya.

Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka yi martani ga bidiyon sun ce wannan ne dalilin da yasa mata basa son furta soyayyarsu ga maza.

Saurari hirar tasu a nan.

Jama'a sun yi martani

@fwesh_habidex ya yi martani:

"Magana ta gaskiya idan har mu samari za mu iya hakuri da tausar zuciyarmu saboda ku mata kun ki amsa tayin soyayyarmu bayan mun ffurta maku, ina ganin ya kamata kuma ku jure sannan ku ci gaba da rayuwa cikin lumana."

@classy_vic ta ce:

"Kara na tauna tsakuwa da na yi wannan. ba da ni ba na zo ina tsara namiji. Ha Allah ya tsare ni."

Kara karanta wannan

“Na Ga Ta Kaina”: Uwa Ta Wallafa Bidiyon Yadda Diyarta Ta Hada Mata Waje, Ta Shige Durowa Ta Yi Zamanta

@iam_trado ta yi martani:

"Wannan abun ya kai mu yi zama na musamman wannan abun ya yi mun ciwo."

@jerrytonwealth ta yi martani:

"Babu wanda ya cancanci a ki shi haka mana. Dan Allah mu zama masu tausayi. Ba laifi bane don baka ji yadda mutane suke ji ba amma dan Allah ka yi shi yadda mai shi ba zai ji an muzanta shi ko tozarta shi ba."

Uban amarya ya yi nasiha mai ratsa zuciya ga surukinsa

A wani labarin kuma, wani uba ya zaunar da surukinsa inda ya yi masa nasiha mai ratsa zuciya kan yadda zai kula da yin hakuri da diyarsa da ya aura masa a matsayin mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng