Na Tausaya Mata: Ango Ya Yi Watsi Da Amarya Yayin da Yake Daddana Waya a Wajen Shagalin Bikinsu

Na Tausaya Mata: Ango Ya Yi Watsi Da Amarya Yayin da Yake Daddana Waya a Wajen Shagalin Bikinsu

  • Bidiyon wani ango yana daddana waya a yayin da ake shagalin bikinsu ya yadu a soshiyal midiya
  • Hankalin angon ya karkata sosai a kan wayar hannunsa yayin da MC ya bukaci amarya ta aiwatar da hakkin aure na farko da ya rataya a wuyanta
  • Mutane da dama da suka garzaya sashin sharhi don fadar ra'ayinsu sun ce abun da angon ya aikata ba daidai bane

Jama'a sun yi cece-kuce a soshiyal midiya bayan bayyanar bidiyon wani ango da hankalinsa ya rabu gida biyu a ranar aurensa da sahibarsa. Ya fi mayar da hankalinsa kan wayarsa fiye da amaryarsa da ma taron.

Shafin farko a bidiyon ya nuno wajen da za a yanka kek din taron. Amaryar ta tsaya a gefen mai gabatar da shirin wato MC yayin da angon ke zaune a kan kujera.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Jama'a Sun Girgiza Bayan Matar Aure ta Haifa Yaro da Maganin Tsarin Iyali a Hannunsa

Ango da amarya
Na Tausaya Mata: Ango Ya Yi Watsi Da Amarya Yayin da Yake Daddana Waya a Wajen Shagalin Bikinsu Hoto: Cila Adjoa Duffuor.
Asali: Facebook

MC ya bukaci amarya ta sauke hakkin aure na farko da ya rataya a wuyanta

MC din ya bukaci amauryar da ta cika hakkinta na aure na farko ta hanyar ciyar da mijinta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hankalin angon ya yi nisa sannan ya karkata ga daddana wayarsa lokacin da MC ya juya don yi masa magana.

Koda dai ba a san da wanene angon ke tattaunawa ba, masu amfani da soshiyal midiya sun yarda cewa amaryar ta cancanci ya bata dukkanin hankalinsa a irin wannan rana mafi muhimmaci a rayuwarsu.

Mutum fiye da 13,000 ne suka kalli bidiyon lokacin da Cila Adjoa Duffuor ya wallafa shi a kan Facebook.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Maame Yaa Yeboaa Asiama ta ce:

"A wannan gabar ne zan bar wajen liyafar bikin da kawo karshen auren da safe. Nkwasiasem sei."

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Dan Najeriya Ya Isa Gaban Rumfar ATM Da Katifa, Matashi, Tukunyar Gas Da Tukunya a Bidiyo

Mawukoenya Yawa Gomashie ta rubuta:

"Jan Kati! Baya ra'ayin auren."

Nha Nah Eyesha ta rubuta:

"Yana yi wa buduwarsa bayani kan dalilinsa na yin auren gaggawa."

Nana Yaw Barimah ta yi martani:

"Ina ganin an bata masa wasansa."

Dee Flow ta ce:

"Na tausayawa amaryar nan. Hakan bai dace ba sam."

An gurfanar da ango kan kara auren mata ta biyu

A wani labarin kuma, mun ji cewa yan sanda sun gurfanar da wani ango a gaban kuliya saboda ya kara auren mata ta biyu bayan ya yi karyar cewa shi din gwauro ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel