Shehu Sani Ya Mayar Da Wani Jinjiri Da Aka Tsinta a Titi Dansa, Jama'a Sun Jinjina Masa

Shehu Sani Ya Mayar Da Wani Jinjiri Da Aka Tsinta a Titi Dansa, Jama'a Sun Jinjina Masa

  • Shehu Sani ya haddasa cece-kuce a tsakanin masu amfani da soshiyal midiyia bayan ya nunawa duniya yaron da ya karba riko
  • A cewar tsohon dan majalisar da ya fito daga jihar Kaduna, an tsinci yaron da ya karba riko ne a bakin titi
  • A halin da ake ciki, yan Najeriya sun jinjina masa a kan wannan abu da ya yi inda masu amfani da soshiyal midiya da dama suka yi masa addu'a

Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya karbi rikon wani yaro da aka tsinta bakin titi. Dan siyasan na Najeriya ya bayyana hakan ne a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 7 ga watan Fabrairu.

A cewarsa, an mika yaron wanda yan sanda suka ceto ga sashin kula da jin dadin jama'a wanda jami'arsa ta mika sa ga gidan marayu.

Kara karanta wannan

Ango Ya Manta Da Amarya a Wajen Shagalin Bikinsu, Ya Mayar Da Hankali Kan Wayar Hannunsa, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Shehu Sani, jinjiri da wata mata
Shehu Sani Ya Karbi Rikon Yaron Da Aka Yasar a Bakin Hanya Hoto: Shehu Sani
Asali: Facebook

Ya rubuta a Facebook:

"Wannan jinjirin yaron an yasar da shi ne a bakin hanya. Yan sanda sun dauke shi sannan suka mika shi ga sashin kula da jin dadin jama'a sannan hukumar ta mika shi ga wani gidan marayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yanzu na zama ubansa kuma na sa masa suna Jordan. Misis Grace da ke gefana ita ce shugabar gidan marayun."

Ya bayyana sunan yaron da ya karba riko a matsayin Jordan.

Nan take wallafar tasa ta haifar da martanoni daga yan Najeriya inda mutane da dama suka jinjina masa.

Jama'a sun yi martani

Christopher Peter:

"Godiya ta tabbata ga Allah, kuma Allah ya maka albarka sannan ya sanya hasken fuskarsa a naka da duk abun da ke dauke da sunanka."

Michael Odeh Anderson:

"Ka yi kokari Sani, akalla dole wani ya dauki wannan zuciya ta tausayin dan adam duk nauyinta."

Kara karanta wannan

Miliyan 1 Nake Biya Duk Shekara: Matashi Ya Baje Kolin Gidan Da Yake Haya a Lagas, Bidiyon Ya Ja Hankali

A halin da ake ciki, wasu sun yi mahawara kan sunan da tsohon dan majalisar ya zabi sanyawa dan.

Uwa ta dauki zafi kan diyarta saboda ta yi aure ba tare da saninta ba

A wani labarin, mun ji cewa ta uwa ta tsinewa yar da ta tsuguna ta haifa saboda ta yi aure ba tare da ta sanar da ita ko ta gayyace ta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel