In Ka ji Gangami da Labari: Jarumi Adam Zango Yace ya Gama Zaman Aure, Ya Saki Bidiyo

In Ka ji Gangami da Labari: Jarumi Adam Zango Yace ya Gama Zaman Aure, Ya Saki Bidiyo

  • Jarumin Kannywood, Adam Zango ya saki bidiyon da ya gigita masoyansa inda yace zai rabu da matarsa da yake aure yanzu don ya gaji da hakuri
  • Ya sanar da cewa, matarsa ta fifita kasuwancinta fiye da aurensa don haka ya gama aure tunda dama yana da zuri'a da yara
  • A cewar jarumin da aka yi wa tambari da auri-saki, yace saboda yana fitacce ba zai cigaba da hadiyar bakin cikin ba yana kannewa saboda masoyansa

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam Zango, ya saki wani bidiyo mai cike da alamomin tambayoyi.

A bidiyon jarumin bai kama suna ba kuma bai yi bayani kai tsaye ba, amma ko shakka babu dada matar da yake aure a halin yanzu yake yi.

Adam Zango da matarsa
In Ka ji Gangami da Labari: Jarumi Adam Zango Yace ya Gama Zaman Aure, Ya Saki Bidiyo. Hoto daga @adamzango
Asali: Instagram

A bidiyon da ya saki mai tsawon mintuna uku, ya bayyana yadda matarsa ta fifita kasuwanci a kan aure amma cikin kwanakin nan za a ji labari, idan kuma an daidaita shikenan.

Kara karanta wannan

Kada Ku Kashe Ni, Zan Tona Asiri: Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Ta Zauce, Bidiyon Ya Girgiza Jama'a

Jarumin bai tsaya nan ba, ya yi rantsuwa kan cewa ya gama aure, kuma ya tabbatar da cewa hakan za ta faru da izinin Allah.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

"Tunda sun zabi kasuwancin da ta ke yi fiye da zaman aurenta ba ni da zabi. A kowanne lokaci daga yanzu, za a ji labari mara dadi. A gafarce ni, wannan shi ne.
"Saboda ina sananne ba zan kashe kaina saboda mabiyana ko masoyana in birge su ba in cigaba da zama da bakin ciki saboda babu yadda na iya.
"Billahil lazi la ila ha illa huwa, har zuciyata da nake maganar nan ba so nake ba. Amma bani da zabi, toh in Allah yasa an daidaita, yayi kyau, idan ba a daidaita ba Allah zai yanke. Babu abinda yafi karfin addu'a.
"Na san dai aure ana yin shi ne saboda raya sunnar Manzon Allah SAW a kuma tara zuria da sauransu. Ina da zuri'a, ina da 'ya'ya, don haka ba ni nayi kaina ba kuma ba na cire rai da rahamar Allah."

Kara karanta wannan

Zuciyar Zinare: Shehu Sani Ya Tsinci Jinjiri a Titi, Ya Mayar Da Shi Dansa

Ya cigaba da cewa:

"Amma ina ganin na gama aure. Da izinin Allah na gama aure, kuma ina rokon Allah ya kare ni daga dukkanin abubuwan da nake gujewa yasa na ke ta yin wannan auren.
"Daga na rabu da mace in sake yin wani auren, wanda in mutum ya zama madaukaki, zai dinga ganin irin wadannan abubuwan da za su dinga bin shi. Idan mutum ba imani ne da shi ba ko kuma addu'a da dauriya, sai ya kauce hanya.
"Kada mutum ya koma ya dinga bin 'yan mata da sauransu, wanda hakan yasa ina rabuwa da mace nake sake yin auren saboda in kaucewa wannan hanyar."

Jarumin ya bayyana cewa, shi ya ke zaune da matarsa kuma shi ya san irin hakurin da ya ke da ita, itama ta san irin hakurin da ta ke yi da shi.

Auren Ado Gwanja ya mutu

A wani labari na daban, auren mawaki Ado Gwanja da matarsa Maimuna Kabir ya mutu a shekarar da ta wuce.

An fara gane ruwan yayi tsami ne bayan da suka goge dukkan hotunan da suka yi tare a shafukansu na Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel