Kannywood: Gaskiyar Dalilin Da Ya Sa Naje Gidan Gala Har Na Taka Rawa Da Yan Mata, Tahir Fage

Kannywood: Gaskiyar Dalilin Da Ya Sa Naje Gidan Gala Har Na Taka Rawa Da Yan Mata, Tahir Fage

  • Jarumin fina-finan Hausa ta Kannywood, Tahir Fage, ya ce lalurar rashin lafiya da rashin kudin magani ne suka sa shi yin rawa a gidan Gala
  • Tahir Fagge ya ce ya nemi taimako a lokacin da yake neman N265,000 na yin magani sai ya samu Rarara, Maishadda da Abdul Amart suka hada masa N55,000
  • Ya ce Ali Nuhu ne mutum guda da ya san zai taimakesa da ya gabatar masa da bukatunsa amma sai yaji nauyin zuwa gare shi

Shahararren jarumin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Tahir I. Fage, ya bayyana dalilinsa na zuwa gidan gala harma ya taka rawa.

Jama’a dai suna ta yamutsa gashin baki bayan bayyanar bidiyon jarumin wanda ya dade ana damawa da shi inda suka dunga sukarsa kan rawa da ya yi da wasu yan mata, cewa sam ba girmansa bane.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Tahir Fage
Kannywood: Gaskiyar Dalilin Da Ya Sa Naje Gidan Gala Har Na Taka Rawa, Tahir Fage Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Sai dai a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, Tahir Fage ya bayyana cewa rashin kudi ne ya same shi, ga rashin lafiya shi ya sa ya je ya yi rawar domin ya samu na magani.

Tahir Fage ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Da farko mutane basa tunanin mecece kaddara a rayuwa, kowaye kai, talaka ne kai, mai kudi ne kai, basarake ne kai, kowaye baka wuce kaddararka ba.
“Lokacin da aka ga wannan fina-finan nawa cewar ina rawa a gidan gala kowa ya san bana gari. Nayi doguwar tafiya, amman mutane basu yi tunani a’a yaya iyalina suke, yarana suna zuwa makaranta? Basa zuwa? Sun ci? Basu ci ba? ba wanda yayi wannan tunanin.
"Amman lokacin da na samu wani ibtila’I ina so in dawo gida, domin duk inda muka hadu da mutum zan ce yi mun addu’a, burina na dawo ga iyalina. Lokacin da na fara kokarin dawowa gun iyalina, sai na samu ciwon zuciya.

Kara karanta wannan

Buhari ya magantu, ya ce akwai wadanda ya kamata suke tallata gwamnatinsa amma ba sa yi

"Duk sanyi sai na fito waje na zauna daga ni sai gajeren wando sai singileti, bana jin wannan sanyin numfashina yana toshewa, bani da kowa sai Allah.
"Lokacin da na dawo, naje asibiti, an gwaggwadani , ana bukatar kudade wanda bani da su. Na san idan nayiwa mutum daya magana da gudu zai dauki wannan kudin ya ban, amman sai naji nauyin shi, Ali Nuhu.
“Lokacin da muka hadu a Kaduna, ya kalli wayar hannuna, ranshi y abaci yace Allah ya sawwake ace muna raye, muna duniyar nan wannan wayar itace a hannunka. A nan take yayi waya aka kawo mun waya. Toh wayar da ya bani da kwana hudu rashin lafiyar nan ta sameni ita na saida. Sai naga ina jin nauyi in koma in sake gaya masa ya taimaka man.
“Lokacin da na fito ina neman taimako, na je gun Rarara, Alhamdulillahi ya bani N20,000, Bashir Mai Shadda ya ban N20,000, Abdul Amart ya ban N15,000, kudin da nake nema a lokacin N265,000.

Kara karanta wannan

A Raba Aurenmu Don Baya Aikin Komai Sai Jajibe-jajiben Fada, Matar Aure Ta Roki Kotu

“Toh ina gida, yau sauki gobe babu lafiya, sai yaran nan suka zo suka sameni cewar dan Allah dan Annabi sun rubuta sunana a matsayin babban bako wand azan kai masu ziyara, za a bude gidan wasa. Nan take suka bani kudi N150,000.
“Ni da nake cikin lalura ta rashin lafiya, naga wannan kudin don in yiwa kaina magani sai na karbi kudin kuma naje. Ina zaune suka gama duk abun da za su yi. Akwai wata tsohuwar waka ta Lilisko, ‘bazar kowa’ wanda ya hauta suka nemi dan Allah don Annabi na kwatantawa yaran saboda basu san wakar ba, sai na hau ta.
Kwana biyu muka yi, nayi kwana daya, a na kwana biyun, aka zo aka sa wakar Hamisu Breaker ‘Mai tafiya’, wannan na nuna masu ga yadda za su yi.

Sai dai kuma, Tahir Fage ya ce ya yafe wa duk wadanda suka zage shi.

Kara karanta wannan

Sai Kace A Kakkara: Dan Najeriya Ya Koka Da Ganin Masaukinsa A Turai, Ya Wallafa Bidiyon Gidan

Burina Na Zama Shugaban Kasar Najeriya Gabaki Daya, Shu’aibu Lawan Kumurci

A wani labari na daban, fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Shu’aibu Lawan wanda aka fi sani da Kumurci ya bayyana babban burinsa a rayuwa.

A wata hira da ya yi da sashin Hausa na BBC a shirin ‘Daga Bakin Mai ita’, Kumurci ya bayyana cewa burinsa a yanzu shine ya zama wani jagora wato bima’ana shugaba.

Sai dai jarumin yace idan Allah ya nufa yana so ya ga ya kai matakin zama shugaban kasar Najeriya ma gabaki daya domin kawo sauye-sauye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel