Burina Na Zama Shugaban Kasar Najeriya Gabaki Daya, Shu’aibu Lawan Kumurci

Burina Na Zama Shugaban Kasar Najeriya Gabaki Daya, Shu’aibu Lawan Kumurci

  • Jarumin fim Shu'aibu Lawan Kumurci ya nuna sha'awarsa na son ganin yana jagorantar mutane a matsayin wani shugaba
  • Kumurci ya ce yana da burin son ganin ya zama shugaba na kasa baki daya duba ga abubuwan da gani a rayuwa
  • Dan wasan ya ce duk da Allah ya yiwa Najeriya baiwa ta arziki da mutane da duk wasu abubuwan more rayuwa, sai ga shi ana rayuwa mai ban tsoro

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Shu’aibu Lawan wanda aka fi sani da Kumurci ya bayyana babban burinsa a rayuwa.

A wata hira da ya yi da sashin Hausa na BBC a shirin ‘Daga Bakin Mai ita’, Kumurci ya bayyana cewa burinsa a yanzu shine ya zama wani jagora wato bima’ana shugaba.

Kumurci
Burina Na Zama Shugaban Kasar Najeriya Gabaki Daya, Shu’aibu Lawan Kumurci Hoto: real_kumurci
Asali: Instagram

Sai dai jarumin yace idan Allah ya nufa yana so ya ga ya kai matakin zama shugaban kasar Najeriya ma gabaki daya domin kawo sauye-sauye.

A cewarsa, yana son rike kanbun shugabanci ne saboda ganin yadda ake rayuwa a cikin Najeriya mai ban tsoro duk da cewar Allah ya albarkaci kasar da arziki, jama’a dama komai na more rayuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da aka tambaye shi game da burinsa a rayuwa sai yace:

“Burikan nawa suna da yawa. Ni burina yanzu naga na zama shugaba wanda na kasa ma gaba daya saboda, irin abubuwan da na dan kakkala a rayuwa da irin yan kasashe da na je wadanda basu kai sun kawo ba amma ga irin yadda suke tafiyar da rayuwarsu amma mu nan Najeriya kuma ga shi muna da arzikin komai, ga shi Allah ya albarkace mu da mutane da jama’a ga kuma komai muna da shi amma irin yadda muke tafiyar da rayuwar tamu sai ka ga abun tsoro.”

Yadda Aka Yi Na Fara Soyayya Da Marigayiya Balaraba Har Ta Kaimu Ga Aure, Lawan Kumurci

A gefe guda, mun ji cewa jarumi Lawan Kumurci, ya magantu a kan soyayyarsa da marigayiyar matarsa, jaruma Balaraba.

A wata hira da ya yi da sashin BBC Hausa a shirin 'Daga bakin mai ita', Kumurci ya bayyana cewa sun fara haduwa ne da jarumar a wajen daukar wani shirin fim inda suka shigo suka tarar da ita a zaune.

Sai dai kuma, jarumin yace ya lura da yadda marigayiyar ta dunga kallonsa amma sai shi ya dauke kai daga wajenta don kada ta tsargu da yawan kallo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel