Sai Kace A Kakkara: Dan Najeriya Ya Koka Da Ganin Masaukinsa A Turai, Ya Wallafa Bidiyon Gidan

Sai Kace A Kakkara: Dan Najeriya Ya Koka Da Ganin Masaukinsa A Turai, Ya Wallafa Bidiyon Gidan

  • Wani dan Najeriya ya koka a soshiyal midiya bayan ya isa kasar Italiya tare da ganin masaukin da aka basa
  • Mutumin wanda ya cika da bakin ciki ya yi korafi kan yanayin wurin yayin da yace ya gaza samun motar bas ko jirgin kasa
  • Da suke martani ga bidiyon, masu amfani da soshiyal midiya sun lallashi mutumin inda wasu suka ba da labarin halin da suka tsinci kansu bayan komawa Turai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Italiya - Wani dan Najeriya wanda ya koma kasar Italiya da zama ya caccaki wata kungiya kan kai shi yankin kakkara a kasar.

A cikin wani bidiyo da ya yadu, matashin ya yi korafin cewa ya biya wata kungiya kudi amma sai suka lamushe kudinsa sannan suka tura shi yankin kakkara.

Gida a Turai
Sai Kace A Kakkara: Dan Najeriya Da Ya Isa Turai Ya Wallafa Bidiyon Gidansa, Jama’a Sun Yi Martani Hoto: @gossipmilltv
Asali: Instagram

Ya wallafa bidiyon dakinsa da kewaye yana mai cewa ya gaza samun jirgin kasa ko motar bas a yankin.

Kara karanta wannan

Ci gaba: Fasihi ya jawo cece-kuce yayin da ya kirkiri 'Wheelbarrow' mai amfani da inji

Da yake magana a bidiyon, matashin ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Jama’a wannan abu ya ishe ni fa. Mutum na murna cewa ya zo Turai. Kalli Turan da mutum ya zo. Kalli gida, kalli unguwar da suka saka ni. Mutum ya fito ma matsala ne. Ban ma ga jirgin kasa ko bas ba. Kalli yankin. Kalli inda suka saka ni a Italiya. Duk wadannan kungiyoyin suna amfani da mu suna tara kudi ne. Kalli inda suka saka ni. Kalla.”

Jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu

_emekajunior ya ce:

“Baba ka yi ka turo kudi ka dawo, ba mu damu ba fa. Kasar waje, kasar waje ce kuma akwai kudi a koina.

Rencepweety8 ya rubuta:

“Yallabai ya danganta da yadda aka yi ka zo faa.. kuma basu tilasta maka zama a nan ba, kana iya yanke shawarar barin wajen ko ka sauya wani wurin cikin sauki.”

Kara karanta wannan

Mata Da Kudi: Yadda Yan Mata Suka Mato Kan Matashi Dan Tsurut Da Ke Tuka Dankareriyar Jeep Cikin Salo A Bidiyo

_solomongrey ya rubuta:

“Baka ji dadi ka ga wajen bacci ba.”

Osdevicesofficial ya ce:

“Duba idan wannan yankin na a google map dan uwa.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel