Pakistan da ke da Nukiliya Ta Tura Sojoji Saudi ana tsaka da Yaki da Houthi

Pakistan da ke da Nukiliya Ta Tura Sojoji Saudi ana tsaka da Yaki da Houthi

  • Rundunar sojin Pakistan ta tabbatar da cewa dakarunta suna Saudiyya domin taimakawa wajen tsaron ƙasar, ƙarƙashin sabuwar yarjejeniyar tsaro da suka yi
  • Kakakin rundunar, Laftanar Janar Ahmed Sharif Chaudhry, ya ce sojojin Pakistan sun daɗe suna Saudiyya, inda suke gudanar da ayyuka ta fannoni daban-daban
  • Wannan na zuwa ne bayan ƙasashen Pakistan, Saudiyya da Turkiyya sun amince da tura dakaru da kayan aikin soji domin ƙarfafa tsaron Saudiyya yayin da take yaki da Houthi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Riyadh – Rundunar sojin Pakistan ta tabbatar da cewa dakarunta suna Saudiyya ƙarƙashin sabuwar yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa da aka sanya wa hannu tsakanin ƙasashen Pakistan, Saudiyya da Turkiyya.

Kakakin rundunar sojin Pakistan, Laftanar Janar Ahmed Sharif Chaudhry, ya bayyana hakan ne a wata hira a gidan talabijin.

Kara karanta wannan

Riyadh: An kai harin da ya girgiza babban birnin Saudiyya

Sojojin Pakistan da Saudiyya
Wasu sojojin Pakistan da Saudiyya a Makkah. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Arab News ta wallafa cewa ya ce sojojin Pakistan sun daɗe suna Saudiyya, inda suke gudanar da ayyuka a fannoni daban-daban na tsaro da aikin soja.

Dakarun Pakistan sun isa Saudi

Chaudhry ya ce ba sabon abu ba ne a samu sojojin Pakistan a Saudiyya, domin ƙasashen biyu sun daɗe suna haɗin gwiwa a fannin tsaro.

“Zan iya tabbatar muku cewa dakarunmu na Pakistan suna can, a Saudiyya. Wannan zan iya tabbatar muku da shi,”

In ji shi.

Da aka tambaye shi ko sojojin Pakistan suna Saudiyya ne ƙarƙashin sabuwar yarjejeniyar tsaro, ya ce sun shafe shekaru da dama suna gudanar da ayyuka a ƙasar ta fannoni daban-daban.

Ya ƙara da cewa yarjejeniyar tsaron da aka kulla ba ta taso daga babu ba, domin ƙasashen Pakistan, Saudiyya da Turkiyya suna da dogon tarihi na hulɗar diflomasiyya, siyasa, soja da zamantakewa.

Yarjejeniyar da aka yi da Saudi

Kara karanta wannan

Siyasar 2027 ta fara daukar zafi, yan daba sun farmaki tawagar kamfen ADC

A ranar 5 ga Oktoba, 2026, Pakistan, Saudiyya da Turkiyya sun amince da ɗaukar matakan gaggawa na tura dakaru da kayan aikin soji zuwa Saudiyya domin ƙarfafa tsaronta.

Al Jazeera ta wallafa cewa an cimma matsayar ne a wani taron gaggawa na kwamitin siyasa da tsaro na ƙawancen tsaron Makkah da aka gudanar a Riyadh.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa, ƙasashen sun yi Allah wadai da hare-haren da aka kai ko aka yi yunƙurin kai wa Makkah da Madina, da kuma hare-haren da suka shafi birane da wuraren fararen hula da tattalin arziki a Saudiyya.

Sun kuma amince da fara aiwatar da yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin tura dakaru da kayan aikin soji bisa ƙa’idojin da aka amince da su.

Shugabannin Saudi da Pakistan
Lokacin da shugabannin Saudiyya da Pakistan suka gana. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Yarjejeniyar ta tanadi taimakon juna idan aka kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen hari

Pakistan, Saudiyya da Turkiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro ta Makkah a ranar 7 ga Agusta, 2026.

An kai hari Madina

A wani labarin, kun ji cewa ƙawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta wajen yaƙi da mayakan Houthi ya zargi ƙungiyar da kai hari kan wata tashar rarraba a Madina.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin hatsarin jirgi, an shiga sansanin sojojin Najeriya an kashe sama da 10

Ƙawancen ya ce harin ya lalata na’urar samar da wuta guda ɗaya, amma bai shafi sauran tsarin wutar lantarkin masallacin Annabi SAW ba.

Daga baya, kungiyar Houthi ta bayar da rahoton hare-haren Saudiyya kan babban birnin Yemen, Sanaa, da wasu yankunan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng