Ba Ni Ku Ke Cutarwa Ba: Lai Mohammed Ya Bayyana Illolin VPN Wajen Hawa Twitter

Ba Ni Ku Ke Cutarwa Ba: Lai Mohammed Ya Bayyana Illolin VPN Wajen Hawa Twitter

  • Ministan yada labarai da al'adu a Najeriya ya bayyana cutarwar dake tattare da amfani da VPN wajen hawa Twitter
  • Ya ce duk masu amfani da VPN wajen hawa Twitter suna cutar da kawunansu da kansu ne kawai ba komai ba
  • Ya kuma bayyana cewa, ya kamata 'yan Najeriya masu ilimi su fara tunanin samar da manhajar da zata maye Twitter

Ministan yada labarai da al'adu a Najeriya ya bayyana illolin dake tattare da amfani da fasahar VPN wajen hawa shafin Twitter a Najeriya.

Shugaban ya yi gargadin cewa, 'yan Najeriya masu hawa Twitter ta hanyar amfani da fasahar ta VPN za su iya tafka asara idan basu kula da kyau ba.

A cewarsa, mai yin haka na sakin bayanansa sakaka ne ga wasu mutane da ba a san ko su wanene ba, lamarin da zai iya kai wa ga sace bayanan sirri na banki da sauran muhimman bayanai.

KU KARANTA: Hotunan yadda jama'ar Zaria suka yi wa 'yan bindiga sallar Al-Qunuti

Ba ni kuke cutarwa ba, kanku kuke cutarwa, Lai Mohammed ya yi gargadin kan amfani da VPN wajen hawa Twitter
Ministan yada labarai da al'adu na Najeriya, Lai Mohammed | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta samo, ministan ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya a shirye take don karfafawa duk wadanda suka yi kokarin samar da wata manhajar da za ta maye gurbin Twitter a Najeriya.

A kalamansa, cewa ya yi:

"Shawara ta ga duk wani mai amfani da VPN shine, ya daina. Saboda, idan mutum ya yi amfani da VPN, yana sakin bayansa sakaka ne, ciki har da bayanan asusun banki.
"Saboda haka idan mutum na amfani da VPN kuma yana jin cewa yana cutar da Lai Mohammed ne, ya sani yana cutar da kansa ne.
"Ina ganin wannan wata dama ce ga 'yan Najeriya masu ilimi da su yi tunanin yadda za su samar da manhajar da za ta maye gurbin Twitter, kuma za mu karfafa hakan gaba dayanmu.
"Mun karbi wasu da suka fara samar da hakan, kuma muna son karfafa musu gwiwa."

Shugaba Buhari ya amince a zauna da jami'an Twitter don sasanci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Babatunde Fashola, Ministan Ayyuka da Gidaje da Abubakar Malami, Babban Lauyan Tarayya, da su tattauna da Twitter game da haramcin shafin na sada zumunta.

Bayan Fashola da Malami, sauran ministocin sun hada da Dr Isa Pantami (Sadarwa da Tattalin Arziki), Chris Ngige, (Kwadago), da Geoffrey Onyeama (Harkokin Waje), Daily Trust ta rahoto.

"Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da rukunin tawagar Gwamnatin Tarayya da za ta zauna tare da Twitter kan dakatarwar da aka yi mata na ayyukan sada zumunta a Najeriya kwanan nan."

KU KARANTA: Bayan tura Burutai Benin, an tura tsoffin hafsoshin tsaro zuwa wasu kasashe

Gwamnatin Buhari ta fadi dalilan da yasa ba za ta amince da ci gaban Twitter ba

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta ce ba a halatta ayyukan Twitter a jerin kafafen sada zumunta na Najeriya ba, The Cable ta ruwaito.

Ta ce ana amfani da Twitter wajen yada labarai "wadanda ke jefa rayuwar 'yan Najeriya cikin hadari da kuma haifar da rashin hadin kai a kasar."

Lai Mohammed, ministan labarai da al'adu, ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya bayyana a gaban majalisar wakilai bisa bincike kan lamarin Twitter.

Biyo bayan dakatar da ayyukan shafin Twitter a kasar, majalisar wakilai ta umarci kwamitocinsa na sadarwa, adalci, bayanai da al'adu, da tsaron kasa da kuma leken asiri na kasa da su binciko yanayin da ya sa aka yanke hukuncin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel