Abubuwa muhimmai masu ƙayatarwa game da Kamala Harris.

Abubuwa muhimmai masu ƙayatarwa game da Kamala Harris.

- Tuni aka fara taya zababben shugaban kasar Amurka, Sanata Joe Biden, murnar lashe zabe

- Jam'iyyar Democrat ta hada Sanata Joe Biden da Sanata Kamala Harris a matsayin mataimakiyarsa

- Kamala Harris, wacce ta kasance ruwa biyu, ita ce mace ta farko da ta taba samun matsayin mataimakiyar shugaban kasa a tarihin Amurka

Kamala Devi Harris tana shirin ɗarewa kujerar Matamakiyar shugaban ƙasa da zarar an rantsar da ita a 20 ga watan Junairu 2021.

An santa a matsayin Sanata a ƙasar Amurka, amma Legit.ng Hausa ta kawo abubuwa guda shida 6 masu ƙayatarwa da ya kamata ku sani game da Kamala Harris.

1. Ita ce mace ta farko da ta kasance mataimakiyar shugaban ƙasa a tarihin Amurka

Yanzu itace mace mafi ƙurewar matsayi a kaf faɗin ƙasar America bayan da tayi nasarar zamowa zaɓaɓɓiyar mataimakiyar shugaban ƙasa, ƙarƙashin inuwar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa,r Amurka Joe Biden.

2. Ita ruwa biyu ce.

Mahaifinta baƙar fata ne. Ta na da asali daga Ƙasar Indiya da kuma nahiyar Afirka. Ita ce mace ta farko Ba'Amurkiya ƴar Afrika kuma ƴar Asiya da ta zamo mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka.

3. Ƙwararriyar Lauya ce.

Ta taɓa zama alƙaliyar gunduma a San Francisco da Kalifoniya kafin ta zama daga bisani ta zama Sanata. Kamala Harris ta riƙe muƙamai da dama ciki har da mataimakiyar shugaban alƙalan gunduma ta ƙasa.

Ta na cikin gwarazan alƙalai 34 na shekarar 2008, acewar Mujallar lauyoyi ta Kalifoniya.

KARANTA: Sojojin Amurka sun kai hari kan 'yan bindigar arewacin Najeriya a kan Ba-Amurke guda daya

Abubuwa muhimmai masu ƙayatarwa game da Kamala Harris.
Joe Biden da Kamala Harris
Asali: Twitter

Baya ga haka sunanta ya na cikin mutane 100 masu faɗa aji a shekarar 2013 a cewar mujallar Times.

KARANTA: Na yi aiki da Gowon, Buhari, da OBJ amma yanzu sai na roki abinci - Kaftin Mai ritaya

4.Ta yi yaƙi da karɓar shawarrar masu gabatar da ƙara wajen yanke hukunci (Proposition 21).

A shekara ta 2000, lokacin Harris ta na mataimakiyar alƙalin gunduma, ta na yanke hukunci akan fashi da makami da cin zarafin jima'i, ta yi fatali da wata doka da zata baiwa masu gabatar da ƙara damar yanke ƙananan hukunci a kotuna.

5. Ta ƙirƙiri ɓuɗaɗɗiyar shari'a

Daya daga cikin muhimman abubuwan da ta cimma a matsayin alƙaliya shine ƙirƙirar kafar shari'a ta yanar gizo wadda zata baiwa mutane damar ganin wainar da ake toyawa. Wannan kafa ta na bada bayanai akan adadin yawan mutuwa da jikkatar masu laifin da suke tsare a hannun ƴansanda, hakan ya ƙara gaskiya da yin aiki yadda ya kamata ga ƴansanda.

6. Tana karatun litattafan ƙirƙira.

Daga cikin littattafan da ta fi sune,The Kite Runner rubutawar Khaleed Hossein da kuma Song of Solomon wallafawar Toni Morrison.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel