An kama 'yan gidan sarautar Saudiyya kan yunkurin hambarar da Sarki Salman

An kama 'yan gidan sarautar Saudiyya kan yunkurin hambarar da Sarki Salman

Wasu manyan 'yan gidan sarautar Saudiyya suna tsare hannun hukumomin kasar a kan zargin da ake musu na cewa suna shirun hambarar da Sarki Salman da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman.

A cewar rahotanni, an tsare daya daga cikin dan uwan sarkin, Yarima Ahmned bin Abdulaziz al Saud da dan uwansa, Yarima Mohammed bin Nayef kamar yadda Sky News ta ruwaito.

Wall Street Journal ta Amurka ta ruwaito cewa an tsare su gidajensu kuma an zargin su da laifin cin amanar kasa.

An kama 'yan gidan sarautar Saudiyya kan yunkurin hambarar da Sarki Salman

An kama 'yan gidan sarautar Saudiyya kan yunkurin hambarar da Sarki Salman
Source: Getty Images

A halin yanzu dai mahukunta kasar ta Saudiyya ba su ce komai a kan rahoton ba.

DUBA WANNAN: An dage auren Suleiman Panshekara da masoyiyarsa 'yar Amurka

Mohammed bin Nayef wanda a baya yana daga cikin masu fada a ji a kasar ya taba rige mukamin shugaban hukumar yaki da ta'addanci kuma ya kasance Yarima mai jiran gado har zuwa 2017 kafin Sarki Salman ya kwace mukamin ya bawa dan sa na fari, Mohammed Ibn Salman.

Yarima mai jiran gadon da ke kula da ayyukan yau da kullum na gwamnatin kasar ya samu yabo daga kasashen Yamma kan sauye-sauye na inganta walwalar al'umma a kasar da ya aiwatar amma wasu kuma suna sukar sa kan yadda ya ke dakile wadanda ba su goyon bayan ra'ayoyinsa.

An soki Mohammed bin Nayef a shekarar 2018 bayan kisar gillar da aka yi wa marubucin Washington Post, Jamal Khashoggi a cikin gidan jakandancin Saudiyya da ke Istanbul.

Masu sukarsa suna zarginsa da hannu cikin aikata kisar amma ya musanta hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel