An Tsinci Gawar Ministan Sufuri Awanni bayan Shugaban Kasa Ya Kore Shi daga Aiki a Rasha
- An tsinci gawar Roman Starovoit, ministan sufuri na Rasha, bayan sa’o’i da aka kore shi daga mukaminsa bisa umarnin Vladimir Putin
- Ana zargin Starovoit da hannu a wawurar dala miliyan 246 da aka ware don kare iyakar Kursk, da kuma wata badakalar ta daban
- Wasu majiyoyi sun ce Starovoit ne ya hallaka kansa saboda damuwar da ya shiga na wadannan zarge-zarge da kuma rasa aikinsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rasha - An tsinci gawar ministan sufurin Rasha, Roman Starovoit, wanda aka kora 'yan sa’o’in da suka gabata, a cikin motarsa a wajen birnin Moscow da harbin bindiga a jikinsa.
A ranar Litinin, masu binciken gwamnatin Rasha suka yi zargin cewa Starovoit ya kashe kansa ne, sa’o’i bayan Shugaba Vladimir Putin ya sauke shi daga mukaminsa.

Source: Twitter
Ministan Rasha da aka kora daga aiki ya mutu

Kara karanta wannan
Kisan Danbokolo: Abin da al'umma suka shirya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya
Sanarwar korar Starovoit da fadar shugaban ƙasa ta fitar da safiyar Litinin ba ta bayyana dalilin sauke shi ba, kuma hakan ya zo ne bayan ya shafe shekara guda kacal a ofis, inji rahoton The Guardian.
Duk da haka, masana harkokin siyasa sun fara danganta saukarsa da binciken cin hanci da ake yi a jihar da ya taba jagoranta a baya.
Wata majiya daga bangaren sufuri ta ce mukamin Starovoit ya dade yana tangal-tangal saboda zargin da ake masa da hannu a wata badakala.
Ana bincike ne kan ko an yi amfani da kuɗin dala miliyan 246 da aka ware tun 2022 domin ƙarfafa iyakar Rasha da Ukraine a yankin Kursk yadda ya dace, ko kuma an wawure wani ɓangare daga ciki.
Ana zargin minista ya hallaka kansa a Rasha
Kwamitin bincike na Rasha, wanda ke kula da manyan laifuffuka, ya ce yana gudanar da cikakken bincike don gano hakikanin yadda Starovoit ya mutu.
Wasu kafafen yada labarai na Rasha sun ruwaito cewa an samu bindigar Starovoit a kusa da gawarsa, wanda ake kyautata zaton ya hallaka kansa ne don radadin halin da yake ciki.

Kara karanta wannan
"Ba a kama shugaban ADC yana cusa daloli a aljihu ba," Dalung ya wanke ƴan APC tas
Amma wasu majiyoyi daga hukumomin tsaro sun ce an same shi da harbin bindiga a kansa a cikin ciyawa kusa da motarsa, kirar Tesla, ba a cikin motar ba kamar yadda aka yi zato a farko.
An bar motar ne a kusa da wani filin shakatawa da ke cikin unguwar da yake zaune a yankin Moscow.

Source: Twitter
Ana zargin Starovoit da rashawa a Kursk
Kamfanin Reuters ya rahoto cewa kafin a naɗa shi ministan sufuri a watan Mayu 2024, Starovoit ya kasance gwamnan jihar Kursk na tsawon kusan shekara biyar.
Watanni uku bayan ya zama minista, sojojin Ukraine suka kutsa cikin yankin Kursk, a hari mafi girma da aka kai cikin yankin Rasha tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu.
A watan Afrilu 2025, aka gurfanar da wanda ya gaji Starovoit a matsayin gwamnan Kursk, kuma mataimakinsa a baya, Alexei Smirnov, bisa zargin wawure kuɗin da aka ware domin tsaro.
An yi zargin cewa an sace kuɗaɗen da aka ware don kare iyakar Kursk, abin da aka ce ya bar yankin Kursk cikin haɗarin hare-haren Ukraine.
Wasu kafafen labarai sun ruwaito cewa Smirnov ya shaida wa masu bincike na gwamnati cewa Starovoit ma yana da hannu a badakalar.
An kama dan Najeriya yana shigarwa Rasha fada
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojojin Ukraine sun kama wani ɗan Najeriya da ke cikin sojojin Rasha a yankin Zaporizhzhia, inda aka ce yana yaƙi a madadin Rasha.
Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya shiga rundunar ne bayan an yi masa tayin rage masa hukuncin dauri saboda laifin safarar miyagun ƙwayoyi da aka kama shi da shi a Rasha.
Majiyoyi sun ce Rasha ta ɗauki dubban ‘yan ƙasashen waje da ke cikin kurkuku ko matsanancin hali, tare da tura su fagen daga don yaƙi da Ukraine.
Asali: Legit.ng
