Hankalin wata mata ya tashi bayan an bar ta da gawa a daki gawar ta tashi da tsakar dare
- Wata mata da ta shafe sama da sa'a takwas da mutuwa ta dawo duniya bayan shafe kusan kwana daya a dakin ajiye gawa
- Matar mai shekaru 81 an gano ta tana rarrafe a tsakiyar dakin da aka ajiye ta tana neman hanyar guduwa daga asibitin
Wata tsohuwa da aka bayyana cewa ta mutu ta tashi bayan tayi kwana daya dakin ajiye gawa na wani asibiti dake kasar Rasha.
Matar mai suna Zinaida Kononova mai shekaru 81 a duniya, an bayyana cewa ta mutu bayan anyi mata tiyata a cikinta a kasar Rasha.
An sanar da danginta, inda suka fara gabatar da shirin jana'izarta. An kaita zuwa dakin ajiye gawa bayan mutuwarta a asibitin dake garin Gorshechensky da misalin karfe 1:10 na dare a ranar 14 ga watan Agusta.
Bayan shafe kimanin awa bakwai a cikin asibitin, wata ma'aikaciya dake lura da gawarwakin ta tsinci kanta cikin tashin hankali, bayan ta ga tsohuwar wacce aka sanar da ita cewa ta mutu tana rarrafe a tsakiyar dakin.
KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin kai Saratu Ya'u matar da ta kashe danta gidan mahaukata
Matar ta fadi a yayin da take kokarin guduwa daga cikin dakin da aka ajiyeta.
Daya daga cikin masu tukin motocin asibitin ya jiyo lokacin da ma'aikaciyar ke yiwa tsohuwar magana akan ta tsaya ta daina shirin guduwa.
Direban ya dauka cewa ma'aikaciyar ta samu tabin hankaline yasa take magana da gawa, amma yana shiga dakin yaga matar ta rikewa ma'aikaciyar hannu tana neman taimako.
Cikin gaggawa aka garzaya da tsohuwar zuwa bangaren taimakon gaggawa na asibitin.
Asibitin sun kira 'yar uwarta mai suna Tatiana inda suka sanar da ita halin da ake ciki, cewa tsohuwar na nan da rai.
Tayi gaggawa ta garzaya zuwa asibitin ta iske likitoci sun zagaye tsohuwar suna duba lafiyarta. Tatiana tayi matukar farin ciki ganin cewa tsohuwar na nan da rai, inda ta tambayi likitan cewa: "Daga yaya haka ta faru?"
Likitocin sun bayyana cewa sun yi kuskuren kai ta dakin ajiye gawar ne sa'a daya da minti ashirin bayan mutuwarta maimakon sa'a biyu kamar yadda doka ta gindaya.
Shugaban asibitin Alexander Vlasov ya ce: "Mun shafe minti 30 a kanta bayan mutuwarta muna kokari wajen tabbatar da ko za ta dawo, amma bata dawo ba."
Daga baya dai an kai tsohuwar matar zuwa babban asibiti na Kursk domin cigaba da lura da ita.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng