Allah Mai Zamani: Bidiyon Yadda Wani Mutum Yayi Cajin Motarsa Kirar Tesla, Sa'a 24 Tayi ta Cika

Allah Mai Zamani: Bidiyon Yadda Wani Mutum Yayi Cajin Motarsa Kirar Tesla, Sa'a 24 Tayi ta Cika

  • Wani matashi yayi bidiyo kan matarsa kirar Tesla domin nunawa jama'a lokacin da take dauka wurin caji a gida da soket
  • Ba kamar wuraren cajinta na kudi ba da take daukar kankanin lokaci, motar ta kwashe sa'o'i 24 tana caji daga 20% zuwa 100%
  • Jama'a da yawa sun yi martani inda suka ce wutar lantarkin $12.8 da ta sha babu tsada idan aka aka kwatanta da zukar mai da motoci ke yi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani mutum yayi amfani da shafinsa na TikTok inda yake bayani kan motarsa kirar Tesla Model 3 kuma yayi bidiyon yadda yake cajin motar mai amfani da wutar lantarki.

Mutumin yace ya so sanin wanne lokacin Tesla din shi zata dauka wurin caji da soket din wutar lantarki a cikin gida.

Tesla Car
Allah Mai Zamani: Bidiyon Yadda Wani Mutum Yayi Cajin Motarsa Kirar Tesla, Sa'a 24 Tayi ta Cika. Hoto daga @ryanjaycowan
Asali: UGC

Ya kashe $12.18 daidai da N5,108.17

Kara karanta wannan

Yajin ma'aikatan wuta: Gwamnati da TCN na rokon kada a sa 'yan Najeriya a duhu

Bayan samun abun cajin motar kuma ya saka a wutar lantarkin gidansa, ta kwashe sa'o'i 24 tana caji inda batirin ya fara daga 20%.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lokacin da mutumin ya koma wurin cajin bayan sa'o'i 15, motar ta kai 55%. Mutumin ya lissafa cewa wutar lantarkin da ta sha kafin ta cika ya kai na $12.8 wanda yayi daidai da N5,108.17.

Kalla bidiyon:

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin martanin jama'a

Alex Aft yace:

"Diesel yafi."

Izak Rebin yace:

"Wanne nisa za ka iya zuwa da ita idan ta cika?"

Michael Sharpe yace

"Boss, ba zan iya zuwa aiki yau ba, motata tana caji."

Yahiko yace:

"Tana kwashe sa'o'i 24 a gida. Cajin Tesla a wurin cajin kudi na kwashe minti 30 kuma dala 5 zuwa 6 ake biya."

Kara karanta wannan

Soyayyar Gaskiya: Bidiyon Auren Kyakkyawar Doguwar Amarya da Wadan Angonta ya Janyo Cece-kuce

Anthony Alfano yace:

"Kawai ka kashe ta, zaka ga ta yi caji da wuri."

Jason Piloton yace:

"Ina mamakin abinda yasa na kalla wannan. Bani ma da kudin siyan mota wacce kowa ya sani."

Zan iya Siyan Namiji da Kudina, In Killace shi a Gidana Kuma in Juya shi Yadda Nake so - Jarumar fim

A wani labari na daban, jarumar fina-finan Nollywood, Nkechi Blessing Sunday, ta buga kirji tare da ikirarin irin dukiyar da ta mallaka inda tace za ta iya siyan namiji, ta ajiye shi a gidanta kuma ta juya shi kamar waina a tanda.

Nkechi Blessing ta bayyana wannan ikirarin ne ta Instagram yayin da ta tattauna da dilan motoci kai tsaye, Chidi Mike CMC.

Ta shiga tattaunawar kai tsaye wacce ta karba bakuncin mutane uku banda Chidi, inda suka yi magana kan aure da kuma ko ya zama tilas mace tayi aure.

Kara karanta wannan

Allah Ya Yi Mun Gamon Katar: Matar Aure Ta Wallafa Hotunan Mijinta Yana Tayata Girki A Icce

Asali: Legit.ng

Online view pixel