Abubuwa 6 da Suka Ja Hankalin Duniya a Kwana 12 na Yakin Iran da Isra'ila

Abubuwa 6 da Suka Ja Hankalin Duniya a Kwana 12 na Yakin Iran da Isra'ila

  • A ranar Litinin shugabana Amurka, Donald J. Trump ya sanar da cewa ya shawo kan yakin da aka gwabza tsakanin Iran da Isra'ila
  • Yayin fadan, Iran ta mayar da martani a wani kazamin harin makamai masu linzami da ya karya tsarin kariyar Iron Dome na Isra'ila
  • A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa da suka faru a lokacin yakin da aka shafe kwanaki 12 ana yinsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Yakin kwanaki 12 da ya barke tsakanin Isra'ila da Iran tun ranar 13 ga Yuni, 2025, ya jawo gagarumar asara da tashe-tashen hankula a gabas ta tsakiya da ma sauran duniya baki ɗaya.

Wannan rikici ya samo asali ne daga harin gaggawa da Isra'ila ta kai wa Iran, wanda daga bisani ya janyo martani daga Tehran.

Kara karanta wannan

Iran ta faɗi yawan mutane da ta rasa da masu raunuka bayan yaki da Isra'ila

Trump ya jawo tsagaita wuta a yakin Iran da Isra'ila
Trump ya jawo tsagaita wuta a yakin Iran da Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Legit Hausa ta yi waiwaye da ranar da Isra'ila ta fara kai hari zuwa Iran domin duba wasu muhimman abubuwa da suka faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan abubuwa shida da suka fi daukar hankali cikin yakin sun hada da:

1. Kisan kwamandoji da masana nukiliyan Iran

Ranar 13 ga Yuni, Isra’ila ta kaddamar da wani mummunan hari da ta kai wa cibiyoyin soji da na nukiliya na Iran.

An ji cewa an hallaka manyan kwamandojin IRGC ciki har da Mohammad Bagheri (Shugaban hafsoshin tsaro), Hossein Salami (Kwamandan IRGC).

2. Iran ta karya Iron Dome na Isra’ila

India Today ta rahoto cewa Iran ta mayar da martani da harin makamai masu linzami masu karfin gaske, wanda ya rinjayi tsarin kariya na Iron Dome da Isra'ila ke amfani da shi.

Ranar 17 ga Yuni, wani sabon dabarar harba makami ya sa na’urorin kariya suka kasa aiki yadda ya kamata, inda makamai suka fada birane kamar Tel Aviv da Haifa na Isra'ila.

Kara karanta wannan

Ana ɓarin wuta da Isra'ila, Shugaban Iran ya yi magana da Shugaba Macron ta wayar tarho

Asibitoci kamar Soroka sun samu lahani, kuma hakan ya fallasa gibin kariya da kasar Isra’ila ke da shi.

3. Kai harin Amurka kan cibiyoyin nukiliya

Amurka ta kai hari kan muhimman cibiyoyin nukiliya na Iran, wanda hakan ya kara tsananta rikicin.

Majiyoyi sun ce Amurka ta yi amfani da manyan jiragen yaki da bama-bamai da suka tarwatsa wasu sassa na cibiyoyin nazarin nukiliyar.

Wannan hari ya janyo matsin lamba daga kasashen duniya da suka soki Amurka kan take dokar kasa da kasa.

4. Harin Iran kan sansanin sojin Amurka a Qatar

Al-Jazeera ta rahoto cewa a ranar 22 ga Yuni, Iran ta kai hari da makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka na Al Udeid da ke Qatar, sansanin da ya fi girma a Gabas ta Tsakiya.

Wannan hari ya biyo bayan harin da Amurka ta kai kan wuraren nukiliya na Iran da suka hada da Fordo, Natanz da Isfahan, da jirage 125 da bama-bamai masu shiga karkashin kasa.

Qatar ta bayyana harin a matsayin take hakkin kasarta, inda ta rufe sararin samaniyarta, yayin da ofishin jakadancin Amurka ya umurci jama’a su zauna a gida.

Kara karanta wannan

'Yar Isra'ila ta rasa ranta sanadin bugun zuciya a harin makami mai linzami daga Iran

5. Zanga-zangar goyon bayan Iran a kasashe

A cikin kasashen Larabawa da dama ciki har da Yemen, Iraq da Lebanon, dubban mutane sun fito zanga-zanga suna nuna goyon baya ga Iran da adawa da Isra'ila da Amurka.

A Yemen, kungiyar Houthi ta bayyana harin da Amurka ta kai wa Iran a matsayin keta dokar kasa da kasa.

6. Iran ta so toshe hanyar ruwan Hormuz

Bayan harin da Amurka ta kai mata, majalisar Tehran ta bukaci toshe hanyar ruwan Hormouz da ya keta ta Iran.

Kasar Amurka ta roki China ta da hana Iran toshe hanyar ruwan domin tasirin da wajen ke da shi a harkar man fetur a duniya.

Hoton ruwan da hanyar Hormuz ke ciki a Iran
Hoton ruwan da hanyar Hormuz ke ciki a Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Legit ta tattauna da Adamu Sa'idu

A tattaunawar da Legit ta yi da wani ma'aikacin banki, Adamu Sa'idu, ya ce babban abin da ya fi jan hankalin shi a lokacin yakin shi ne cigaban da Iran ta samu a fannin kimiya.

Adamu ya ce:

Kara karanta wannan

Tarihi bai manta ba: China ta tunawa duniya yadda Iran ta buga gwagwarmaya a baya

'Na yi mamaki matuka yadda naga Iran na harbo makamai daga sama. Lallai hakan ya ja hankali na.
"Hakan ya kara tabbatar min da cewa ilimi na iya fitar da mutum a kunya."

Iran ta yaba wa sojojinta bayan tsagaita wuta

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Iran ta yi bayani na musamman bayan amincewa da tsagaita wuta.

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa sun amince da tsagaita wuta kuma suna godiya ga sojojinsu.

Hakan na zuwa bayan kokarin da Amurka ta yi wajen ganin ta shawo kan yakin da ya barke tsakanin Iran da Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng