Sarkin Saudiyya, Salman ‘Dan Abdulaziz ya na kwance a gadon asibiti

Sarkin Saudiyya, Salman ‘Dan Abdulaziz ya na kwance a gadon asibiti

- An kwantar da sarki Salman ‘dan Abdul'aziz na Saudiyya a asibiti

- Sarkin ya na kwance ne a wani asibiti da ke birnin Riyadh a kasar

- Rahotanni sun ce ana yi wa Dan Abdul'aziz gwaje gwaje a mafitsara

Sarki Salman ‘Dan Abdul'aziz na kasar Saudi Arabiya ya na kwance a wani asibiti sakamakon larura da ya samu a mafitsararsa.

Rahotannin da su ke fitowa daga gidajen jaridun kasar Saudiyya a ranar Litinin, sun tabbatar da cewa an kwantar da sarkin mai shekaru 84 a asibiti.

SPA, Kamfanin dillacin labarai na kasar Saudi Arabiya ya bayyana cewa an dai kwantar da Salman Abdul'aziz ne a wani asibiti da ke babban birnin Riyadh.

Bayan rahotannin cewa Sarki Salman ‘Dan Abdul'aziz ya na fama da kumburi a mafitsararsa, babu wani labari da aka samu game da halin shugaban.

KU KARANTA: Saudi za ta gina matatar mai a Najeriya

Sarkin Saudiyya, Salma ‘Dan Abdulaziz ya na kwance a gadon asibiti
Yariman Saudiyya, Mohammed 'Dan Salman ‘Dan Abdulaziz
Asali: Getty Images

Yanzu haka ana yi wa Sarkin na Saudiyya, kuma mai kula da masallatan musulunci masu tsarki da ke biranen Makkah da Madina gwaje-gwaje a asibiti.

Dattijon Sarkin ya yi shekaru biyar ya na mulki, amma ana ganin babban ‘dansa kuma yarima mai jiran gado watau Mohammed ‘dan Salman ya ke jan ragamar kasar.

Sakamakon rashin lafiyar da ta kama Sarkin, Firayim Ministan kasar Iraki, Mustafa al-Kadhimi, ya dakatar da ziyarar da ya yi niyyar kai wa zuwa kasar Saudi.

“Ganin muhimmancin ziyartar muda kuma neman ganin an ci nasara, shugabanni da mutanen Iraki sun dauki matakin dakatar da wannan ziyara.” Inji Yarima Faisal Farhan Al Saud.

Kafin hawansa mulki, Salman ya rike kujerar Yarima mai jiran gado a kasar Saudiyya, kuma ya shafe shekaru fiye da 50 ya na kan kujerar gwamnan babban birnin Riyadh.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel