Kungiyar CAN Ta Shawarci Isra'ila da Falasdinu da Su Koma Teburin Sulhu Don Zaman Lafiya

Kungiyar CAN Ta Shawarci Isra'ila da Falasdinu da Su Koma Teburin Sulhu Don Zaman Lafiya

  • Kungiyar CAN a Najeriya ta ba da shawara da a koma teburin sulhu don samun zaman lafiya mai dorewa
  • Kungiyar na magana ne kan rikicin da ke wakana tsakanin kasashen Isra'ila da Falasdinu wanda ya yi sanadin rayuka da dama
  • Ta shawarci hukumar kula da aikin hajji na Kiristoci da su dakatar da jigilar maniyyatan har zuwa lokacin da za a samu zaman lafiya

FCT, Abuja - Kungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) ta nuna damuwa kan gwabza yaki da ake tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Kungiyar ta shawarci dukkan bangarorin biyu da su koma teburin sulhu don samun zaman lafiya, The Nation ta tattaro.

CAN ta shawarci Isra'ila da Falasdinu su koma teburin sulhu don samun zaman lafiya
Kungiyar CAN ta yi martani kan rikicin Isra'ila da Falasdinu. Hoto: CAN.
Asali: Facebook

Meye kungiyar CAN ta ce kan Isra'ila da Falasdinu?

CAN ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa Isra'ila na ba bazata wanda ya yi sanadin mata da kananan yara wanda ke kawo matsala a zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Dira Jihar Arewa, Ya Aike da Kakkausan Saƙo Ga Yan Ta'adda, Ya Ba Su Zaɓi 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya bayyana haka a yau Laraba 11 ga watan Oktoba cikin wata sanarwa.

Mista Daniel ya ce ba sa goyon bayan duk wani matakin da zai jawo rasa rayuka na 'yan Adam ko a wane kasa kuma ko wane addini su ke.

Sanarwar ta ce:

"Kungiyar CAN ta shiga damuwa na rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinu da ke sanadin rasa rayukan mutane da dama a yankunan.
"CAN na damuwa musamman yadda rikicin zai shafi Najeriya da kuma maniyyata daga kasar."

Wane shawara CAN ta bayar kan Isra'ila da Falasdinu?

Ya kara da cewa:

"Mafi yawan Kiristoci a Najeriya na gudanar da aikin hajj a Jerusalem da sauran wurare masu tsarki, wannan rikici zai iya jefa rayukan 'yan kasar cikin hatsari."

Shugaban ya shawarci dakatar da jigilar maniyyatan zuwa Isra'ila a dai-dai wannan lokaci har sai an samu zaman lafiya, Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Isra'ila Ta Yi Wa Tinubu Alkawarin Ba Da Kariya Kan Rikicin Kasar Da Falasdinu, Ta Fadi Dalilai

Ya kara da cewa wannan rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinu na iya kawo matsala ga addinan Najeriya inda ya shawarci malaman addinai da su yi hudubar zaman lafiya ga mabiyansu.

Kungiyar CAN ta taya Musulmai bikin Maulidi

A wani labarin, Kungiyar Kiristoci a Najeriya, CAN ta taya al'ummar Musulmai murnar zagayowar ranar Maulidi a kasar.

Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya bayyana haka inda ya bukaci su yi amfani da bikin wurin yin addu'a ga kasar don samun zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel