Firayim Ministan kasar Côte d'Ivoire Amadou Gon Coulibaly ya rasu

Firayim Ministan kasar Côte d'Ivoire Amadou Gon Coulibaly ya rasu

A ranar Laraba, 8 ga watan Yuli, 2020, mu ka samu labari daga Aljazeera cewa Firayim Ministan kasar Côte d'Ivoire, Amadou Gon Coulibaly, ya rasu ya na da shekara 61.

Amadou Gon Coulibaly shi ne Firayim Ministan Côte d'Ivoire tun 2017, kuma ‘dan takarar jam’iyya mai mulki a zaben da ake shirin yi a watan Oktoban bana.

Gon Coulibaly ya rasu ne kwanaki kadan bayan dawowarsa daga kasar Faransa inda ya yi jinyar rashin lafiya na kusan tsawon watanni biyu a wani asibiti.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, rashin lafiya ya kama Amadou Gon Coulibaly ne a lokacin da ya ke tsakiyar gudanar da taron ministoci da sauran jami’an gwamnati.

Daga nan ne aka sheka da shi zuwa wani asibiti da ke cikin kasar inda a can ya rasu. Mai magana da yawun bakin shugaban kasa Alassane Ouattara ya bayyana wannan a jiya.

KU KARANTA: An samu mutane 460 masu COVID-19 a Najeriya

Firayim Ministan kasar Côte d'Ivoire Amadou Gon Coulibaly ya rasu
Marigayi Gon Coulibaly Hoto: BBC
Asali: Facebook

Dama can an taba yi wa Amadou Gon Coulibaly aiki a cikin zuciyarsa a shekarar 2012. Sharararren 'dan siyasar ya dade ya na fama da larurar rashin lafiya.

Mutuwar wannan dattijo mai shekaru 61 ya jefa kasar yammacin Afrikar a cikin rudun siyasa domin kuwa kafin mutuwarsa, shi ne ke rike da tutar takara a jam’iyya mai-ci.

Coulibaly wanda ke rike da kujerar Firayim Minista ya yi niyyar tsayawa takarar shugaban kasa ganin cewa shugaba Alassane Ouattara bai da sha’awar sake neman tazarce a zaben 2020.

Kasar CIV wanda a da ake kira Ivory Coast ta dawo daidai ne a ‘yan shekarun bayan nan. An yi wani gajeren yakin basasa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3, 000 a kasar.

Ouattara ya fitar da jawabi ya na kiran Coulibaly wanda su ka yi gwagwarmaya tare ‘karamin kani kuma ‘da. Ya ce: "Na jinjinawa ‘dan kishin kasa, mai tsantsar amana da kaunar al’umma.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel