Tashin Hankali Yayin Da Mai Tsaron Lafiyar Minista Ya Bindige Shi Har Lahira

Tashin Hankali Yayin Da Mai Tsaron Lafiyar Minista Ya Bindige Shi Har Lahira

  • Wani minista a ƙasar Uganda ya gamu da ajalinsa bayan sojan da ya ke tsaron lafiyar sa, ya bindige shi har lahira
  • Lamarin dai ya auku ne lokacin da ministan ya ke ƙoƙarin shiga motar sa, domin tafiya wajen aiki
  • Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa sojan wanda shi ma ya halaka kan sa, ya yi ƙorafin rashin biyan sa haƙƙoƙin sa

Uganda - Ƙaramin ministan ƙwadago, samar da ayyukan yi da harkokin masana'antu na ƙasar Uganda, Kanal Charles Okello Engola, ya mutu har lahira bayan ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyar sa ya bindige shi.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa, sojan mai tsaron lafiyar ministan, ya bindige shi ne a ranar Talata, 2 ga watan Mayun 2023.

An halaka minista har lahira a Uganda
Karamin ministan ƙwadago na Uganda, Charles Enanga Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar ƴan sandan Uganda, Fred Enanga, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne lokacin da ministan ya ke ƙoƙarin shiga mota domin tafiya wajen aiki.

"Ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyar ministan ne ya yi harbin, wanda ya kuma yi ta harbe-harbe a kurkusa. Daga nan sai ya tsere ya bar wajen zuwa cibiyar kasuwanci ta Kyanja kan titin Ring Road, inda ya shiga wani shagon gyaran gashi sannan ya bindige kan sa." A cewar Enanga

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa, tuni har an fara bincike, inda ya ƙara da cewa:

"Mun tura ƙwararru zuwa wajen da lamarin ya auku, waɗanda za su yi amfani da ƙwararrun kayan aiki na zamani domin gano haƙiƙanin dalilin da ya sanya aka yi kisan."

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, sojan ya yi ƙorafin rashin biyan sa albashin sa da rashin kyautata masa, kafin ya bindige kan sa, cewar rahoton The Cable.

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Wata Budurwa a Kudancin Kaduna

A wani rahoton na daban kuma, wasu ɓata gari da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun yi awon gaba da wata matashiyar budurwa a jihar Kaduna.

Miyagun sun bi tsakar dare ne suka yi awon gaba da budurwar a garin Ikulu na masarautar Ikulu, wacce ke a ƙaramar hukumar Zangon Kataf cikin Kudancin jihar Ƙaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel