Magana Tayi Nisa, An Sanar da Shugaban Amurka Yadda Aka ‘Murde’ Zaben Najeriya

Magana Tayi Nisa, An Sanar da Shugaban Amurka Yadda Aka ‘Murde’ Zaben Najeriya

  • The Atlantic ta fito da budaddiyar wasikar da Chimamanda Adichie ta rubutawa shugaban Amurka
  • Marubuciyar ta soki zaben da aka yi a Najeriya, ta nemi Joe Biden ya guji taya Bola Tinubu murna
  • Adichie take cewa yarda da sakamakon zaben Najeriya zai bata daraja da mutuncin Amurka

America - Wata jarida mai suna The Atlantic da ke kasar Amurka, ta wallafa budaddiyar wasikar da Chimamanda Adichie ta aikawa Joe Biden.

Wasikar Chimamanda Adichie wanda marubuciya ce ‘Yar Najeriya da ke zaune a Amurka, ba ta kunshe da komai sai korafi kan zaben kasar na 2023.

Chimamanda Adichie ta soki damukaradiyyar Najeriya, ta kalubalanci yadda Amurka ke aiko da sakon taya murna ga wanda ya ci zaben da aka yi.

The Guardian ta rahoto cewa shahararriyar marubuciyar ta nuna cewa an ci amanar mutanen kasarta da suka kada kuri’a a zaben sabon shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Zolayi Gwamnoni Da Suka Sha Kaye A Zaben Sanata, Ya Aika Sako Ga Yan Siyasa

"Magudi da aka yi da gan-gan"

A cewar Adichie, an samu hujjoji da suka nuna an saba doka a zaben da hukumar INEC ta gudanar, ba a daura sakamakon zabe a yanar gizo a lokaci ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba a iyaka murdiya aka tsaya ba, wasikar wannan Baiwar Allah ta ce yadda aka tafka magudin ya zama tamkar cin fuska da raina tunanin mutane.

Shugaban Amurka
Joe Biden da Muhammadu Buhari Hoto: govbusinessjournal.ng
Asali: UGC

Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyya mai-ci aka sanar a matsayin wanda ya yi nasara, amma Misis Adichie take cewa babu abin da ake yi sai fushi da takaici.

Wasikar ta ce babu wadanda zaben bai yi masu dadi ba kamar matasa, ta ce za a dauki shekara da shekaru ba a huce takaicin wannan abin da ya faru ba.

Kira ga gwamnatin Amurka

Game da yadda aka ji sanarwa ta fito daga Sakataren gwamnatin Amurka, ana taya Bola Tinubu murna, Adichie ta ce bai kamata Amurka su jahilci lamarin ba.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Dawo Ɗanye, APC Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Da Wani Babban Jigo

Da an yi bincike, marubuciyar ta na ganin za a tabbatar da da-gan-gan aka kitsa magudi a zaben, sai ta bukaci Joe Biden ya tashi tsaye, ya ceci damukaradiyya.

The Cable ta ce wasikar ta kare ne da kira ga Biden na Amurka da ya barranta kan shi daga zaben, ya ce Amurka za ta bata kimarta idan ta gaskata sakamakon.

A ciki sai da aka yi magana a kan Tinubu da shari'ar da aka yi da shi a Amurka.

Maganin masu fita cin rani

A makon nan labari ya zo cewa Gwamnatin Najeriya na nmean takawa likitoci masu tserewa kasashen waje birki domin a daina fama da karancin ma'aikatan lafiya.

Majalisar wakilan tarayya na kan yin dokar tilastawa likitocin yin aikin shekaru biyar a kasarsu kafin a iya ba su cikakken lasisi da har za su nemi aiki a ketare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel