Idan Kun San Wata Ba Ku San Wata Ba: FG Na Daf Da Takaita Zirarewar Likitoci Fita Waje Aiki

Idan Kun San Wata Ba Ku San Wata Ba: FG Na Daf Da Takaita Zirarewar Likitoci Fita Waje Aiki

  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya na son yin gyara ka dokar Likitoci don tilasta wa likitocin da aka horas a Najeriya yin aikin shekara biyar kafin su iya fita hijira
  • Yan majalisa sun bayyana ra'ayoyinsu kan batun inda wasu suka nuna rashin amincewa yayin da wasu kuma sun ce akwai hikima a yin dokar suka kuma bada dalilai
  • Daga karshe, kudirin dokar ya wuce karatu na biyu a yayin da Femi Gbajabiamila, Kakakin Majalisar ya bada damar a jefa kuri'a a kanta

FCT, Abuja - Majalisar Tarayyar Najeriya ta fara aikin yin gyara ga dokar Likitoci da Likitocin Hakori domin hana likitocin da aka horas a Najeriya yin hijira kasashen waje, Premium Times ta rahoto.

Gyaran wanda Ganiyu Johnson (APC, Legas) ya gabatar, yana bada shawarar duk likitocin da aka horas a Najeriya ya zama dole su yi aiki na shekara biyar a kasar kafin a basu cikakken lasisin aiki.

Kara karanta wannan

Ahaf: Gwamnatin Buhari ta gano kasashen Turai na daukar nauyin ta'addanci, sun sha suka

Majalisar Dokokin Tarayya
FG Na Daf Da Takaita Zirarewar Likitoci Fita Waje Aiki. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Yayin mahara kan gyaran da ake son yi wa kudirin a ranar Alhamis, Mista Johnson ya ce idan ana son adalci ya kamata likitocin da aka horas a kasar, suka amfana da kudin harajin yan kasa yayin horas da su, 'to saka wa kasarsu'.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu yan majalisan ba su yarda da neman tilastawa likitocin aikin shekara biyar ba

Uzoma Abonta (PDP) ya nuna rashin amincewarsa da kudirin, yana mai cewa hakan take hakkin likitocin ne na zuwa duk inda suke so.

Shima Mark Gbillah (LP, Benue) ya nuna rashin yardarsa da kudirin, ya bukaci a sake nazari kansa gabanin a gabatar da shi.

Dokar da ake son yi ba ta take hakkin likitoci ba - Gbajabiamila

Kafin ya ba wa yan majalisa daman yin mahawara kan kudirin, Kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila ya ce dokar da aka gabatar ba take hakkin likitocin bane saboda sashi na 45 na kundin mulkin kasa na 1999 ya bawa gwamnati ikon janye wasu hakoki a wasu yanayi.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Gama Shirin Janye Tallafin Fetur, An Karbo $800m Daga Bankin Duniya

Ya ce:

"Bari in yi karin haske kan batun take hakkin bil adama da aka tada.
"Idan ka tafi sashi na 45(1) na kundin tsarin mulki, ta baka kawar da kai daga hakkin bil adama a wasu yanayi.
"Daya daga cikin wadannan yanayin shine lafiyar kasa. Idan gwamnati na ganin don kiyayye lafiyar kasa a saka wannan dokar, toh ba mu take hakkin kowa ba."

Yan majalisar sun amince kudirin ya wuce karatu ta biyu da Gbajabiamila ya bukaci a kada kuri'a kan batun, The Punch ta rahoto.

Hijira zuwa kasar waje

Duk da karancin kwararrun ma'aikatan lafiya a kasar, Najeriya na cigaba da rasa kwararrun ma'aikatan lafiyarta da suka hada likitoci, masana kimiyyan magani da malaman jinya.

Wani zaben jin ra'ayi da NOIPolls ta shirya tare da Nigeria Health Watch a 2017 ya nuna cewa kashi 88 cikin 100 na likitocin Najeriya na neman guraben aiki a kasashen waje.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Tsaida Ranar Kammala Manya-Manyan Ayyukan da Buhari Ya Tattago

A bara, Kungiyar Likitoci, MDCAN, ta ce mambobinta fiye da 100 sun bar kasar cikin watanni 24.

Likitocin Sun Bar Mutanen Karkara Sun Tare A Legas Da Abuja, Ngige

A wani rahoton, Chris Ngige, Ministan Kwadago ya ce akwai isasun likitoci a kasar amma mafi yawancinsu sun tare ne a biranen Legas, Abuja da Fatakwal.

Ngige ya koka cewa likitocin sun bar mutanen karkara inda nan ma ana bukatar ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel