Ka amsa buƙatun masu zanga zanga tun da wuri - Majalisar tarayya ga Buhari

Ka amsa buƙatun masu zanga zanga tun da wuri - Majalisar tarayya ga Buhari

- Wasu yan majalisun tarayya sun bukaci Buhari da ya dauki matakin gaggawa kan zanga-zangar da ke gudana

- Sun nemi Buhari ya fara da biya wasu daga cikin bukatun masu zanga-zangar

- Har ila yau sun yi tir da budewa masu zanga-zangar lumanan wuta da jami'an tsaro suka yi

Wasu sanatoci da mambobin majalisar wakilai sun fara kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dau mataki ta hanyar aiwatar da wasu daga cikin bukatun masu zanga-zangar EndSARS.

Yan majalisun sun yi kiran ne a wani jawabin hadin gwiwa a ranar Laraba, dauke da sa hannun sanatoci hudu da yan majalisar wakilai 35.

Jawabin na dauke da sa hannun Francis Ottawa Agbo (PDP Benue), Sanata Olu Adetunbi, Sanata Michael Opeyemi Bamidele, Sanata Tolu Odebiyi da Dr Surajudeen Ajibola Basiru da sauransu.

Sun bayyana cewa a sannu-sannu sun bibiyi zanga-zangar EndSARS da matasa ke yi a fadin Najeriya a tsawon makonni biyu.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Miyetti Allah ta bankaɗo wanda ke ɗaukar nauyin Zanga-zanga

Ka amsa buƙatun masu zanga zanga tun da wuri - Majalisar tarayya ga Buhari
Ka amsa buƙatun masu zanga zanga tun da wuri - Majalisar tarayya ga Buhari Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

Sun yi korafi a kan kashe-kashen da aka yi a birane da dama da suka hada da Jos, Kaduna, Abuja, Benin da Lagas, Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Mun lura cewa a yan baya-bayan nan, wannan shine zanga-zanga mafi girma da ya hada matasan Najeriya a fadin kasar ba tare da banbancin kabilanci ko addini ba.

“Mun lura cewa zanga-zangar ya wuci na neman a rushe rundunar SARS,” in ji su.

Yan majalisun sun yi Alla-wadai da amfani da karfi da harbin masu zanga-zanga wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka da jikkata mutane.

“Babu wata hujja da zai ba jami’an tsaro da ake biya da kudin masu biyan haraji damar kashe masu zanga-zangar lumanan.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon yadda ƴan sandan Faransa suka ga akushin tsafi a harabar ofishin jakadancin Nigeria da ke ƙasar

“Muna kira ga shugaban kasa da ya yi jawabi ga kasar sannan ya dauki matakai masu karfi na biyan bukatun masu zanga-zangar,” in ji su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel