Wata sabuwa: Miyetti Allah ta bankaɗo wanda ke ɗaukar nauyin Zanga-zanga

Wata sabuwa: Miyetti Allah ta bankaɗo wanda ke ɗaukar nauyin Zanga-zanga

- Wani dan siyasa daga yankin kudu maso yamma ne ke daukar nauyin zanga-zangar EndSARS, a cewar kungiyar Miyetti Allah

- Shugaban kungiyar makiyayan, Alhaji Bello Abdullahi Bodejo, ne yayi zargin a wata hira

- Bodejo, wanda ya bayyana cewa da fari ya yi farin ciki da gangamin, ya ce zanga-zangar na da mummunan ajanda na son kar da gwamnati mai ci zuwa kasa

Kungiyar Fulani makiyaya a Najeriya, Miyetti Allah, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yiwa zanga-zangar EndSARS da ke gudana rikon kazar kuku, cewa gangamin wani shiri ne na durkusar da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da yake magana a wata hira da jaridar The Sun, Shugaban kungiyar, Bello Abdullahi Bodejo, ya ce duk da an gaskata manufar zanga-zangar, ta zarta lokacinta.

Shugaban Miyetti Allah, wanda ya bayyana cewa ya yi farinci lokacin da zanga-zangar ta fara, ya tabbatar da cewa mambobin kungiyar da dama sun dandana kudarsu a hannun rundunar SARS da aka rushe.

Wata sabuwa: Miyetti Allah ta bankaɗo wanda ke ɗaukar nauyin Zanga-zanga
Wata sabuwa: Miyetti Allah ta bankaɗo wanda ke ɗaukar nauyin Zanga-zanga Hoto: Daily Sun
Asali: UGC

Bodejo ya bayyana cewa kamata yayi a ce masu zanga-zangar sun dakatar da gangaminsu sannan su bar tituna tunda gwamnati ta amsa bukatunsu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Osun ya bai wa masu satar kayan tallafi wa'adi, ya sanar da abinda za su iya fuskanta

Ya ci gaba da bayyana cewa rashin komawar masu zanga-zanga gidajensu ya nuna cewa “akwai wani boyayyen ajanda a zanga-zangar.”

A cewar Shugaban kungiyar Miyetti Allah, “wani dan siyasa a kudu maso yamma ne ke daukar nauyin zanga-zangar.”

Da yake ci gaba da magana, Bodejo ya bayyana cewa ana kama Fulani makiyaya a kan dalilai marasa tushe yayinda jami’an SARS ke neman a biya kudi tsakanin "N500, 000 da N600, 000 na beli kafin su saki mutum; sun matsawa mutanenmu.”

“Akwai wani boyayyen ajanda a zanga-zangar. Ga dukkan alamu, ba wai yan siyasa bane kawai, illa wani dan siyasa da ya matsu daga yankin kudu maso yamma ne ke daukar nauyin wannan gangami. Wannan ne dalilin da yasa muka ki yin shiru, sannan muka yanke shawarar sanar da kasar abunda ke faruwa saboda mafi akasarin mutane basu san ma’anar abunda ke faruwa ba.

KU KARANTA KUMA: Shugabanni su farka, mulkin kama-karya ne yake fusata matasa - Okorocha

“Ba zanga-zanga bane kuma; wani dan siyasa da ya matsu wanda ke ganin cewa ba zai kai labari ba a 2023 shine ke kada gangar nan ga matasanmu.”

A gefe guda, Cif Olusegun Obasanjo ya yaba ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan jawabin kasa da yayi kan zanga-zangar EndSARS.

Tsohon shugaban kasar ya kasance daya daga cikin shugabannin Najeriya da ke raye wadanda Buhari ya gayyata zuwa wani taro na yanar gizo a ranar Juma’a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel