Bidiyon yadda ƴan sandan Faransa suka ga akushin tsafi a harabar ofishin jakadancin Nigeria da ke ƙasar

Bidiyon yadda ƴan sandan Faransa suka ga akushin tsafi a harabar ofishin jakadancin Nigeria da ke ƙasar

- Yan Najeriya sun yi martani ga wani bidiyo na yan sandan Faransa a shafin soshiyal midiya

- Jami’an yan sandan sun gano katoton akushin tsafi a harabar ofishin jakadancin Najeriya a kasar Faris

- Yan sandan na Faransa sun shiga rudani yayinda suke kokarin sani menene ke cikin akushin

Bidiyon wasu jami’an yan sandan Faransa cikin rudani yayinda suka ga wani akushin tsafi a harabar ofishin jakadancin Najeriya a kasar Faris ya bayyana.

Bidiyon wanda ya shahara a yanzu haka a yanar gizo, ya nuno jami’an yan sandan suna duba akushin yayinda suke kokarin fahimtar abunda aka zuba a ciki.

Akushin cike yake da kayan tsubbu, sai dai kuma, babu wanda zai iya cewa ga abunda ke ciki.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi da sata a banki a Legas

Bidiyon yadda ƴan sandan Faransa suka ga akushin tsafi a harabar ofishin jakadancin Nigeria da ke ƙasar
Bidiyon yadda ƴan sandan Faransa suka ga akushin tsafi a harabar ofishin jakadancin Nigeria da ke ƙasar Hoto: @opeyemi_aiyeola
Asali: Instagram

An gano jami’an yan sandan suna zagaye kayan asirin yayinda suke magana cikin harshen Faransa.

Jarumar Nollywood, Opeyemi Aiyeola ta wallafa bidiyon a shafinta na Instagram inda yan Najeriya suka yi sharhi a kai.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Ƴan ta'adda sun kashe ƴan sanda biyu yayin da suka bankawa ofishin rundunar wuta a Oyigbo

iamfunminuro: “Menene dalilinsu na kira yan sanda? Jami’an yan sandan turai basu san komai game da ebo ba.”

elizabeth.ogundare.52: “Wannan ya shige ni sosai fa.”

ms_chiomax: “Sun san menene tsafi?”

lordchitu: "lol. Yan Najeriya!”

A wani labari na daban, Gwamnatin Amurka tace za ta rufe ofishin jakadancinta dake Legas na kwanaki 2 sakamakon zanga-zangar da aketa yi a jihar.

Ta kuma shawarci 'yan kasar da su tabbatar sun kiyayi wuraren da ake zanga-zangar don gudun matsala.

Duk da dai ofishin jakadancin Najeriya basu nuna wanda suke goyon baya ba akan al'amarin zanga-zangar ta shafinsu na Twitter ba. Sun dai sanar da rufe ofishin nasu dake Legas na tsawon kwanaki 2.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel