Kasar tukunya ya zama magani?

Kasar tukunya ya zama magani?

- An sake gano wata tsohuwar tukunyar a kusa da ta farko, inda mutane na cigaba da zuwa inda aka gano tukunya mai tsohon tarihi

- Jama’a na dibar kasar da zummar magani, domin tukunyar na da girma da zurfin da za ta ci buhun shinkafa 20 a lokaci guda

Kasar tukunya ya zama magani?
Sabuwar tunkunyar da aka gano a kusa da tsohuwar

 

Mutane na cigaba da tururuwa zuwa kauyen Rummawa Rangaza a jihar Kano a inda aka sake hako wata tukunya mai girma gaske a kasa.

Jama’ar da ke tururuwa ba wai kawai suna zuwa don ganewa idanunsu takunyar ba ne, yawanci suna zuwa ne domin dibar kasar tunkunyar da wasu suka camfa da cewa, ta na warkar da cututtuka musamman annobar zazzabi da ake fama da ita a jihar.

Kasar tukunya ya zama magani?
Kasar tukunya ya zama magani?
Dandazon matan da ke dibar kasar tukunyar domin magani

Tukwanen wadanda aka kimanta shekarunsu da sama da dari, na da girman da za a iya sa kimanin buhun shinkafa 20 ba su cika su ba, saboda girma da kuma zurfin su.

Wani mazaunin yankin Muttaqa Eto o Dawakin Dakata ya ce, yawan mutane da ke zuwa wurin ya ba su mamaki matuka, musamman mata da ke dibar kasar domin yin magani. Ya kuma ce, a tukunya ta farko an gano wata karama a ciki, yayin a ta biyun a gano wata ‘yar buta.

Kasar tukunya ya zama magani?
Kasuwa ta budewa masu zirga-zirgar abin hawa, a inda safarar mutane masu neman ganin kwa-kwaf

Masana tarihi na cewa, ana samar da irin wadannan tukwane ne a zamanin da, ko a matsayin matattarar ruwa, ko na kafin gari a inda ake tsibbace-tsibbace, ko kuma na tsimin magani domin tsaron gari musamman a lokacin da ake yake-yake.

Wasu magina ne suka ci karo da tukunyar a lokacin da suke haka ramin fandishon gina wani gida a yankin, wanda hakan ya sa suka sanar da hukumomi bayan kokarinsu na hagowa da kuma fito da tukunyar ya ci tura.

Hukumomin kula da adana kayayyakin tarihi na jiha da na gwamnatin tarayya da ke jihar ba su soma aikin hako tukwanen ba domin alkintawa, sai dai an ce an ga wani bature ya zo wurin ya na bincike, ya kuma ce da akwai sauran tukwanen guda bakwai a wajen.

An an taba samun irin wadannan tukwane a garin Ririwai a karamar hukumar Doguwa a shekarun  1980, da kuma a unguwar Nomans land, da ke yankin Sabon gari a karamar hukumar Nassarawa, a cewar wani jami’I na hukumar adana kayyakin tarihi na kasa da ke Gidan Makama, ba su kai girman wacce aka gano a yanzu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng