Raguna: Da alama layya zata gagari talaka wannan Sallah

Raguna: Da alama layya zata gagari talaka wannan Sallah

- Yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke fara haramar shirye-shiryen sallar Laiya

- Yanzu haka farashin Raguna na kara tashin gwauron zabi, haka kuma jama’ar Najeriya na cigaba da kokawa game da matsatsin rayuwa.

Kamar yadda ake sa ran gudanar da sallar ne a farkon makon gobe, sai dai kuma sallar na zuwa ne cikin wani halin tashin gwauron zabi da Raguna sukayi a bana. Majiyar mu data ziyarci babbar kasuwar garin Jimeta ta shaida mana karancin masu sayan ragunan.

A cewar sarkin Tike Alhaji Mohammad Yalo, wanda shine mataimakin shugaban kungiyar fataken dabbobi na Jimeta, yace hasashe na nuna musu cewa bana akwai karancin Raguna domin yanzu haka akan sayesu ne domin fitar da su kasar Kamaru. Alhaji Mohammad yayi kira ga jama’a da cewa duk mai niya ya hanzarta ya sayi nasa ragon da wuri.

Yayin da matsalar rayuwa ke kara yawa a wasu sassan Najeriya, kamar yadda rahotanni ke cewa wasu ‘yan baranda suka fara shiga wasu ‘kauyuka suna saye amfanin gonar da aka noma, abin da yasa wasu magidanta ke kokawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng