Wani aure da wasu yan biyu sukayi mai kayatarwa.

Wani aure da wasu yan biyu sukayi mai kayatarwa.

Aure dai yana da kyau sosai, amman wannan kalan auren kuwa ba'a iya bayyanawa saboda tsabar kyawunsa. Saboda kuwa aurene akayi wanda yan biyu suka auri yan biyu.

Wani aure da wasu yan biyu sukayi mai kayatarwa.

Sunan yan matan dai Teyolla da kuma Keyolla Loux. Wanda suke karkashin kulawar wasu masu yada addinin kirista, wa'anda sune suka rikesu amman basu suka haifesu ba, wa'anda suke gudanar na addininsu a tsibirin Marshall. Wanda anan ne suka sami ainihin mahaifiyar yan matan akan ta basu yan matan su koyi harkar addini a wajan su domin su sami rayuwa mai kyau, wanda daga baya mahaifiyar tasu ta amince da bukatar tasu dasu tafi dasu USA inda anan ne su suke.

Wanda anan ne yan matan suka samu abokan rayuwar su wanda suma yan biyune masu suna Eric da Shawn, wanda suma suna taimakawa a cikin cocin, a inda zamu iyacewar sakaiya ce, domin kuwa abokai ne sosai amman daga baya sun rabu a inda kowa yaje gurin nashi bautar a wurare daban daban. Allah ya kara dawo dasu suka hade.

Haka ya taba faruwa a Haiti, alokacin da akayi girgizan kasa, inda dukansu sukaje amatsayin masu sadaukarwa wanda suma yan biyu ne, suma suka hadu da yan biyu mata wanda kowa ya amince da bukatar kowa nayin aure, wanda daga baya suka auri junan su.

KU KARANTA : Shugaban kasar Togo yazo Lagos domin bunkasa kasuwanci

Samari suna da zabi akoda yaushe, sannan kuma yana da kyau ka nemi aure wajan iyayen Yarinya domin suzo su tayaka murnan aure ka. Kunde ga yadda wadannan suka ribanya jin dadin su zuwa biyu, wannan shirin nasu yayi kyau sosai.

Muna tayaku murna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel