Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

  • Sanata Uba Sani ya musanya abin da wasu ke fada game da tattalin arzikin Najeriya
  • ‘Dan Majalisar yace tattalin arzikin bai sukurkuce ba, ya yi kira a ba CBN hadin-kai
  • Sanatan na Kaduna ya yaba da irin kokarin da ake yi, yace a daina bata sunan kasar

Abuja - Shugaban kwamitin da ke kula da harkar banki, inshora da hukumomin tattalin arziki a majalisa, Uba Sani, ya yi magana a kan tattalin arzikin kasar nan.

A ranar Lahadi, 3 ga watan Oktoba, 2021, Sanata Uba Sani ya shaida wa manema labarai cewa a halin yanzu tattalin arzikin Najeriya bai kama hanyar ruguje wa ba.

Leadership ta rahoto Sanatan yana wannan bayani, ya yi kira ga mutane su daina kashe wa kasar kasuwa.

Uba Sani wanda yake wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya yi gargadi cewa yawan sukar tsare-tsaren bankin CBN yana taba tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

A cewar Sanatan, akwai bukatar a yarda da aikin da babban bankin kasa na CBN yake yi, a kuma nemi hadin-kai da sauran masu zuba hannun jari a kasashen waje.

Sanatan Kaduna
Sanata Uba Sani a Majalisa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanatan na jam’iyyar APC yake cewa shugaban majalisar dattawa, Dr. Ahmed Lawan, ya bukaci kwamitocinsu su ba gwamnati duk wata gudumuwa da take bukata.

‘Yan majalisar za suyi bakin karfinsu domin ganin an farfado da darajar Naira da tattalin arzikin kasar ta hanyar tallafa wa CBN, da duk wasu ma’aikatun gwamnati.

Jaridar ta kuma rahoto Sanata Sani yana cewa duk kokarin da gwamnan CBN zai yi, dole kowa ya tashi tsaye domin ganin an tashi komadan tattalin arzikin Najeriya.

Sani yake cewa babban bankin CBN ya yi abin a yaba wajen bada tallafin COVID-19 domin hana tattalin arzikin Najeriya girgiza a sakamakon mummunar annobar.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

“Ana cikin wani hali ne a yanzu, ana bukatar a dauki matakan farfado da tattali. Ba za mu shiga sahun masu ganin laifin wasu ba, sai dai mu bada gudumuwa.” - Uba Sani

Sanusi II yace tattalin arziki zai durkushe

Bayanin Uba Sani ya zo ne bayan an ji tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammad Sanusi II, yana cewa tattalin arzikin Najeriya ya kusa durkushe wa.

Tsohon sarkin Kano ya tabbatar da cewa kazar da ke yi wa Najeriya kwai ta na daf da sheka wa lahira. Ba wannan ne karon farko da Sanusi II ya fadi irin haka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel