'Yan sanda sun cafke tsageru 13 da ake zargi 'yan bindiga ne kuma barayin shanu a Katsina

'Yan sanda sun cafke tsageru 13 da ake zargi 'yan bindiga ne kuma barayin shanu a Katsina

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina sun cafke wasu 'yan bindiga da dama a wasu sassan jihar
  • An kama ciki har da matashi mai shekaru da ke da hannu dumu-dumu a fashi da makami
  • Wannan na zuwa ne yayin da jami'an tsaro ke cci gaba da samun nasara kan ta'adda a jihar

Katsina - Rundunar ‘yan sanda a jihar atsina ta cafke mutane 13 da ake zargi da hannu a fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane da safarar makamai da kuma ta’addancin kan 'yan jihar da ba su ji ba su gani ba.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar Katsina, Gambo Isah ne ya bayyana hakan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Isah ya ce kamun wadanda ake zargin ya kasance wani bangare na nasarorin da rundunar 'yan sandan jihar ta samu a baya-bayan nan a ci gaba da yaki da miyagun laifuka da aikata laifuka a jihar.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama mutumin da ke taimakawa masu garkuwa karɓar kuɗin fansa

'Yan sanda sun cafke tsageru 13 da ake zargi 'yan bindiga ne kuma barayin shanu a Katsina
'Yan sandan Najeriya | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Depositphotos

A cewarsa:

"‘Yan sanda a Katsina sun samu nasarar cafke wani matashi dan shekara 30 da ake kira DAN OGA, na kauyen Sabaru, karamar hukumar Tsafe, Jihar Zamfara, wani sanannen dan bindiga.
“A lokacin da ake gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa yana karkashin ikon wani mai suna Chairman, wani sanannen dan bindiga da ke boye a cikin dajin Zamfara.
”Ya furta cewa yana da hannu a harin da aka kai kauyen Unguwar Dodo, na karamar hukumar Tsafe ta Zamfara inda aka fasa shaguna aka sace kayan abinci da sauran kayayyaki.
“Wanda ake zargin ya kuma ambaci Hakimin unguwarsu da sauran mutane a cikin wadanda suke tare da shi.2

Mai magana da yawun 'yan sandan ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa wanda ake zargin na sansanin Bammi Tsoho ne, a dajin Dumburum, sanannen shugaban yan bindiga wanda ke cikin jerin mutanen da rundunar ke nema ruwa a jallo da ke boye a dajin Rugu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi

Ya kuma bayyana cewa bisa ga sahihan bayanan sirri, rundunar ta samu nasarar cafke wani matashi dan shekara 35 a kauyen Unguwar Tambaya a karamar hukumar Dutsinma, sanannen mai garkuwa da mutane kuma mai leken asiri ga 'yan bindiga.

Mista Isah ya kara da cewa:

“An kama wanda ake zargin a wani lokaci da ya gabata dangane da laifin fashi da makami da sata wanda har yanzu yana gaban shari’a a Babbar Kotun kuma an bayar da belin sa."

Ya kara da cewa a ranar 23 ga Satumba, rundunar ta kuma yi nasarar cafke wani matashi dan shekara 19, wanda ake kira ‘Duru’, na kauyen Garin-Inu, karamar hukumar Batsari ta jihar.

“Wanda ake zargin ya furta cewa yana da hannu a hare-haren da aka kai kan Bugaje, Rayi da sauran kauyuka karamar hukumar Batsari da Jibia sun sace dabbobi da yawa da ba a san adadinsu ba kuma sun yi garkuwa da mutane."

Kara karanta wannan

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

Ya ce an kama sauran wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da safarar makamai, sata, fashi da taimakon 'yan bindiga.

'Yan sanda sun bata, an kona mutum da ransa a sabon harin 'yan bindiga a Sokoto

Kwanaki biyu bayan kashe jami'an tsaro a sansanin soji a Sokoto, 'yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kai harin ne a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar, ranar Laraba 29 ga watan Satumba, inda suka kona wani mutum da ransa kana 'yan sanda suka tsere.

A Sabon Birnin ne 'yan bindigar suka kashe akalla jami'an tsaro 17 a farkon makon nan.

Daily Trust ta tattaro cewa an sace mutane 27, ciki har da mata da yara daga Gatawa, wani gari a Sabo Birni.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, dan majalisar mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Gabas a majalisar dokokin jihar, Sa’idu Ibrahim, ya ce a yanzu haka ‘yan bindigan suna kai hare-hare kan hukumomin tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sandan Zamfara suka kama 'yan bindiga 69 da masu haɗa baki da su

Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara

A wani labarin, alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.

Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.

Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel