Rahoto: Yadda Bagudu ya wawuri biliyoyi tare da boyesu a ketare tun zamanin Abacha

Rahoto: Yadda Bagudu ya wawuri biliyoyi tare da boyesu a ketare tun zamanin Abacha

  • Gagarumin binciken Pandora Papers ya bayyana Gwamnan Kebbi, Abubakar Bagudu ya handami tarin dukiya tun zamanin mulkin Abacha
  • Biliyoyin naira da ya diba ya hankada su Turai domin shi, matarsa, iyalansa da kaninsa, Ibrahim Bagudu su dinga amfana da ita
  • Sai dai Gwamnan ya musanta inda lauyansa ya ce wannan dukiya ta halastacciyar hanya aka same ta

Gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi a halin yanzu ya zama abun magana kan dukiyar da ake zargin ya tara ta cikin dukiyar da Janar Sani Abacha, tsohon shugaban kasan Najeriya ya diba.

Akwai rahotanni kan yadda Bagudu ya dinga amfani da wasu kamfanoni wurin wawurar dukiya tare da hankada ta Turai amma gwamnan ya musanta, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tonon asiri: Yadda Stella Oduah ta wawuri N5b, ta siya katafaran gidaje a London

Rahoto: Yadda Atiku Bagudu ya wawuri biliyoyi tare da boyesu ta hannun Abacha
Rahoto: Yadda Atiku Bagudu ya wawuri biliyoyi tare da boyesu ta hannun Abacha. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wani sabon sakamakon bincike mai suna Pandora Papers, daya daga cikin gagarumin bincike da aka taba yi na harkallar kudi a duniya, an bankado yadda ya tura wakilai Singapore domin neman masa mafaka ga abinda tsarin shari'ar Amurka ke neman kwacewa.

A binciken, an gano cewa akwai makuden kudi wanda suke daga cikin biliyoyin daloli da Bagudu ya taimaka wa iyalan Sani Abacha suka sace daga baitul malin Najeriya.

"Kamar yadda Farrer and Co., wanda tsohon kamfanin doka da ya wakilci gidan sarautar Turai, ya ce a kasar Singapore, wadanda suka taimaka wa Bagudu su ne Asiaciti Trust, wani fitaccen kamfani da yayi kaurin suna wurin taya jama'a boye kazamar dukiya a duniya."

Ana zargin kanin Bagudu da hannu dumu-dumu a cikin al'amarin

A ranar 23 ga watan Fabrairun 2010, wakilan Bagudu da suka hada da dan uwan shi, Ibrahim Bagudu tare da wani lauyan London, Ben Davies daga kamfanin Byrne and Partners, sun hadu da jami'an Asiaciti inda suka yi rijistar adanar kazamar dukiyar a sirrance ta bangaren man fetur wanda zai amfane shi da iyalansa.

Kara karanta wannan

Ba na cikin matsananciyar bukatar takarar shugabancin kasa, Gwamnan Bauchi

A shekarar 1997, shekaru 13 kafin nan, Bagudu ya mika kazamar dunkiyar hannun Trust and Ridley Group, wadanda suka adana ta kuma ya ke amfana da ita. Amma a 2010, ya bukaci karbar dukiyar domin mika ta ga Asiaciti saboda a lokacin ba su iya juya kamfanin baya kuma suna tsoron rasa dukiyar baki daya.

"A nan ya tabbatar da cewa duk wanda zai sake damka wa dukiyar, dole ne ya zamanto wanda zai iya bada umarni kan dukiyar a bi," Premium Times tace.

Boko Haram sun gurgunta mulki a Neja, sun kayyade shekarun aurar da 'ya'ya mata

A wani labari na daban, 'yan ta'addan Boko Haram sun addabi jama'a mazauna karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja da su dinga aurar da 'ya'yansu mata a shekaru 12.

Daily Trust ta ruwaito cewa, mazauna yankin da lamarin ya shafa sun ce 'yan ta'addan sun ba su umarnin cewa kada su kuskura su saurari wata hukuma.

Kara karanta wannan

Fallasar handama: An matsa wa Buhari lamba kan ya bincike Bagudu, Obi da sauransu

Daya daga cikin mazauna yankin kuma daga cikin matasan Shiroro mai suna Bello Ibrahim, ya sanar da Daily Trust hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: