Gwamnatin Jihar Kaduna ta sallami ma'aikata 286 daga aiki
- Hukumar ruwa da jihar Kaduna ta sallami ma'aikata 286
- Hakan na zuwa ne bayan bincike da tantancewa da aka yi
- An gano da dama masu takardun bogi da wasu laifukan daban-daban
Kaduna - Hukumar Ruwa na Jihar Kaduna, KADSWAC, ta sallami a kalla mutan 286 daga cikin ma'iaikatanta bayan kidaya da tattance satifiket da ta yi a baya-bayan nan.
Sanusi Maikudi, Babban manajan KADSWAC, ne ya tabbatar da hakan yayin wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Talata a Kaduna, Daily Nigerian ta ruwaito.
Dalilin korar ma'aikatan?
Ya ce hukumar ta sallami ma'aikatan ne saboda gabatar da takardun kammala karatu na bogi bayan ta tafi makarantun da suka yi ikirarin sun kammala ta tabbatar cewa na bogi ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mr Maikudi ya ce:
"Yayin atisayen, mun iya gano ma'aikatan bogi, wadanda shekarunsu ya kai na ritaya, wadanda rashin lafiya ba zai iya bari su yi aiki ba da wadanda aka dauka ba bisa ka'ida ba.
"Wasu daga cikinsu kuma takardun kammala karatu na bogi gare su wanda laifi na, don haka muka kore su."
Ya ce binciken da aka yi ya nuna rashawa da ake tafkawa, cin amana, cin hanci da bannatar da kudade da ma'aikatan hukumar ke yi.
A cewarsa:
"An yi bincike, wadanda ba su da laifi an kyalle su, yayin da wadanda aka samu da laifin kuma an hukunta su dai-dai da laifinsu wasu kuma aka kore su yayin da wasu aka musu ritaya."
Mr Maikudi ya ce wannan atisayen ya zama dole duba da muhimmancin da ruwa ke da shi da kuma tsaftace muhalli.
Hukumar ruwa na da muhimmanci sosai wurin samar da ruwa da tsaftace muhalli.
"Gwamnatin jihar ta kashe kudi sosai a bangaren don habbaka shi, abin da ake bukata shine kwararrun ma'aikata masu izzar son yin aiki domin amfanin dukkan masu ruwa da tsaki.
Babban aikin mu shine kare lafiyar al'umma da hana mutane kamuwa da cuttuka domin fiye da kashi uku cikin hudu na cututtuka da mutane ke kamuwa da su na da alaka da ruwa," in ji shi.
A kan daukan ma'aikata, Mr Maikudi ya ce bayan kammala aikin ruwan Zaria, za a dauki masu gadi 50, ma'aikata kwararru bakwai da kuma ma'aikata biyar a bangaren kasuwanci.
Ya ce:
"Ana shirin daukan ma'aikata 150, 100 cikinsu za su kasance wadanda suka kammala digiri ne a bangarori daban-daban na aikin ruwa, yayin da 50 cikinsu kuma masu gyaran ruwa ne da za a bawa horaswa bayan an dauke su."
A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu
A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.
Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.
Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng