Daga bisani, NAF ta dauka alhakin yi wa farar hula ruwan wuta a Yobe

Daga bisani, NAF ta dauka alhakin yi wa farar hula ruwan wuta a Yobe

  • Rundunar dakarun sojin saman Najeriya ta tabbatar da hannunta cikin yi wa mazauna kauyen Buhari luguden wuta a Yobe
  • Kamar yadda kakakin NAF ya bayyana, ya ce tabbas an hango 'yan ta'adda a kusa da yankin, lamarin da yasa aka yi luguden wutan
  • Da farko kakakin rundunar ya musanta labarin sakin ruwan wuta, lamarin da yasa wasu suka mutu yayin da wasu suka raunata

Yobe - Rundunar sojin sama ta Najeriya ta bayyana cewa ita ke da alhakin sakin wa jama'ar kauyen Buhari da ke karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe bama-bamai ta jirgin yaki bisa kuskure.

Daily Trust ta ruwaito yadda a kalla mazauna kauyen takwas suka rasa rayukansu, wanda Air Commodore Edward Gabkwet, mai magana da yawun rundunar ya musanta da farko.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisa ya musanta kwatanta IPOB, 'yan Yarbawa da Boko Haram

Daga bisani, NAF ta dauka alhakin yi wa farar hula ruwan wuta a Yobe
Daga cikin jama'ar da suka jigata sakamakon luguden da jirgin NAF ya yi wa jama'a a Yobe. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin martani kan lamarin, Gabkwet ya ce:

"Wannan wallafar ta Twitter babu gaskiya a cikin ta gaba daya. A karon karshe da NAF ta kai samame ta jirgin yaki a jihar Yobe ba karamar hukuma Yunusari ba ne. Kuma ranar 5 ga watan Satumba ne. Babu bam ko wani makami da aka wurga. Nagode."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma a takardar da aka fitar a ranar Alhamis, mai magana da yawun NAF ya sanar da cewa sojin saman sun yi wasu harbe-harbe, Daily Trust ta wallafa.

Ya ce wasu mayakan ta'addanci na Boko Haram ne aka yi niyyar samu, inda ya alakanta wallafar sa ta farko da cewa ba a wurga bam ba.

"Bayan rahotannin sirri da aka samu kan 'yan Boko Haram a wurin rafin Kamadougou da ke Yobe. An tura jirgin yakin Operation Hadin Kai bayan an yi mishi bayanin cewa akwai 'yan ta'adda da ke tsakanin iyakar Najeriya da Nijar."

Kara karanta wannan

Rundunar sojin saman Najeriya ta fara bincike kan barin wuta da jirgin yaki ya yi kan fararen hula a Yobe

"A yayin da jirgin yakin ke aiki wurin kudancin Kanama, an hango kaiwa da kawowar 'yan ta'addan Boko Haram a yayin da jirgin da ya ke shawagi.
“Kamar yadda ya dace, matukin jirgin ya yi harbe-harbe. Akwai muhimmancin a gane cewa yankin har yanzu akwai al'amuran 'yan Boko Haram. Amma kuma rahotannin da NAF ta samu shi ne an jefa wa wasu farar hula harbin kuma sun mutu yayin da wasu suka raunata."

Rikicin APC: Kamata ya yi a dawo da ni kan hanya idan na kauce, Gwamnan Gombe

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce a dawo da shi hanya idan an ga ya kauce. Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin yin tsokaci dangane da rikicin shugabancin jam’iyyar APC a jihar.

Ya musanta batun samun rikicin shugabanci tsakanin sa da tsohon gwamnan jihar, Danjuma Goje, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Jirgin yaki ya yi luguden wuta kan al’umman gari? Rundunar soji ta yi martani kan rahoton

Gwamnan ya sanar da BBC cewa, ba ya da wani takun-saka tsakanin sa da Goje, sai dai wajibi ne kowa ya yi biyayya ga tsarin shugabancin jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel