Alamu 7 da mutum zai gane jikinsa na bukatar ruwa wanda mutane basu sani ba

Alamu 7 da mutum zai gane jikinsa na bukatar ruwa wanda mutane basu sani ba

-70% na jikin dan adam ruwa ne, hakan yana nuna cewa jikin yana bukatar ruwa sosai don cigaba da rayuwa

-Jinin jiki ma 83% dinsa ruwa ne, sannan sai kwakwalwa ma tana da 76% nata wanda shima ruwa ne

70% na jikin dan adam ruwa ne, hakan yana nuna cewa jikin yana bukatar ruwa sosai don cigaba da rayuwa. Haka zalika jijiyoyin jiki da kwada ma duk kusan ruwane. Jinin jiki ma 83% dinsa ruwa ne, sannan sai kwakwalwa ma tana da 76% nata wanda shima ruwa ne.

Jiki yana rage ruwa ta hanyar numfashi zufa da kuma fitsari, saboda haka yake da kyau ka ringa shan ruwa dayawa a kowace rana. Masana ma sun bayyana cewa ana bukatar ka ringa shan kofin ruwa 6 zuwa 8 a kowace rana, amma yawancin mutane basu wuce biyu.

KU KARANTA KUMA: Hukumar yan sanda ta kamo makamai 948 a jihar Sokoto

Maza ana bukatar susha lita 3 ta ruwa ko kofi 12, mata kuma bukatar su ringa shan lita 2.2 ko kuma kofi 9 na ruwa. Rashin isashshen ruwa a jiki yana kawo tsanewar jiki, wanda ake ganewa ta hanyar alamun.

Alamu 7 da mutum zai gane jikinsa na bukatar ruwa wanda mutane basu sani ba
Alamu 7 da mutum zai gane jikinsa na bukatar ruwa wanda mutane basu sani ba

1. Bakin Fitsari

Shine abu na farko dake nuna maka cewa jikinka na bukatar ruwa sosai. Fitsari na mai lfiya zaka ganshi dorowane mai haske. Idan baka dauki shan ruwa da muhimmanci ba zai kawo maka matsala a kodar ka, saboda zata ringa fitar da mataccen jini ta nan mai dama shine yasa zakaga fitsainka yayi duhu.

2. Ragowar Fitsari

Duk mutum mai lafiya yana yin fitsari a kalla sau 6 ko 7 a cikin awowi 24. Amma idan baka sha ruwa yanda ya kamata ba jikin bazai mayar da ruwan da ya fitar ba cikin lokaci, wanda keda koda ta bushe bayan anaso koda yaushe ta kasance akwai ruwa mai dama cikinta.

3. Shakuwa

Babbar alamace dake nuna tsanewar jiki, kuma yawanci, zakaga idan ka yawaita shan ruwa zai magance maka matsalar. Idan bakasha isashshe ba zakaga kana yin kasha mai tauri, kuma idan babu isashshen ruwa a jikinka to jikin zai jawo ruwa daga jijiyonka don ya cigaba da aiki.

4. Bushewar jiki

Yawanci mata suna kashe kudi wurin sayen man jiki, wanda ke sanya laushin fata. Dr. Diana Howard tace, tsanewar jiki shine ke kawo canzawar launin jiki da kaikayi. Wani lokaci zakaga jikin ya bushe har fata na tsagewa da jini yana fita ta fatar

5. Yunwa da kuma Karin nauyin jiki

Jikin dan adam inji ne mai dabara, amma kuma bazai iya banbance tsakanin yunwa da kishirwa ba. Shiyasa akeso ka ringa kula da lafiyarka ta hanyar shan ruwa yanda ya kamata da kuma kula da kibar jikinka. Dakaji yunwa anaso kasha ruwa kafin kaci abinci, idan ka cigaba da jin yuwar bayan minti 15 sai kaci abinci.

6. Kishi ko bushewar baki

Kishirwa babbar alamace a jikin dan adam wadda ke nuna cewa jikin na bukatar ruwa. Bushewar baki alamace da akafi saurin gane cewa mutum na jin kishi, shiyasa akeso ka yawaita shan ruwa a kowace rana.

7. Ciwon kai

Idan baka sha isashshen ruwa ba, jikin yana janyo ruwa daga jijiyoyinka, kamar yanda muka riga muka fada, saboda yana kokarin tara ruwan da ya kamata yayi aiki dashi. Haka zalika yana jawo ruwa daga kwawalwa wanda hakan yakesa kwakwalwar tana rabuwa da kasha kai wanda ke sanya ciwon kai. Kuma rashin ruwa a jiki yana rage yawan jinin dake jikin mutum.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel