Jirgin yaki ya yi luguden wuta kan al’umman gari? Rundunar soji ta yi martani kan rahoton
- Rundunar sojin sama ta yi magana kan jita-jitan da ta dabaibaye wani jirgin yaki da ya jefa bama -bamai cikin kuskure a wani kauye a jihar Yobe
- Mai magana da yawun rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, ya musanta cewa rundunar ce ke da alhakin faruwar lamarin
- Gabkwet ya bayyana cewa aikin NAF na karshe a jihar Yobe bai kasance a karamar hukumar Yunusari ba
Yobe - An yi watsi da rahoton da ke ikirarin cewa wani jirgin sama mallakar rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ya kashe mazauna wani gari a jihar Yobe.
Legit.ng ta tattaro cewa mai magana da yawun NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya yi wannan karin haske a cikin wani rubutu da aka yada a shafin Facebook na Aso Rock Villa a ranar Laraba, 15 ga Satumba.
Ions Intelligence, wata kungiyar tsaro ta yi zargin cewa jiragen yakin NAF yayin da suke aikin yaki da Boko Haram da ISWAP sun jefa bana-bamai bisa kuskure a Kauyen Buhari da ke karamar hukumar Yunusari wanda ya kashe mazauna yankin da dama tare da jikkata wasu.
Gabkwet ya ce rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta karya ne, ya kara da cewa aikin karshe da rundunar NAF ta yi a Yobe ya gudana ne a ranar Lahadi 5 ga watan Satumba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya yi bayanin cewa aikin na makamai ne kuma ba a yi amfani da bam ko makami mai linzami ba.
'Yan ta'addan Boko Haram sun koma dajin Kaduna – DSS ta ankarar da sauran hukumomi
A wani labarin, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta nemi hukumomin tsaro a Kaduna da su kasance cikin shirin ko ta kwana kan yiwuwar kai hare-hare, Sahara Reporters ta ruwaito.
Ta bayyana cewa shugabanni da dakarun kungiyar ‘yan ta'adda na Boko Haram sun koma wani daji a Kudancin Kaduna daga Dajin Sambisa.
A cikin wata sanarwa da jaridar Peoples Gazette ta gani, an ce yan ta’addan sun kaura daga dajin Sambisa a jihar Borno zuwa dajin Rijana da ke karamar hukumar Chikun ta Kaduna.
Asali: Legit.ng